Sojoji sun kubutar da mutum biyu daga hannun ’yan bindiga a Taraba

Sojoji da taimakon ‘yan sa sun ceto akalla mutane 6 da ‘yan bindiga suka sace a Jihar Kebbi.

Sojoji sun kubutar da mutum biyu daga hannun ’yan bindiga a Taraba

Taraba a taswira

Dakarun rundunar sojin kasa na Najeriya sun samu nasarar kubutar da wasu mutum biyu daga hannun masu garkuwa da mutane a garin Jalingo na Jihar Taraba.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamandan runduna ta 6, Birgeriya Janar Frank Etim ya fitar.

A cewar sa, sun samu nasarar ne a safiyar ranar Lahadi, lokacin da suka samu bayanan yadda bata-garin suka addabi yankin.

Ya ce sun kama biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen, yayin da sauran suka tsere.

A bayan nan ne sojoji da taimakon ‘yan sa kai suka yi nasarar ceto akalla mutane 6 da ‘yan bindiga suka sace tare da shiga da su dajin da ke Karamar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.

Daraktan tsaro na Ofishin Gwamnan Kebbi, Abdulrahman Usman ya shaida wa manema labarai cewa dukkanin mutanen 6 an sada su da iyalansu bayan nasarar ceto su daga hannun ‘yan bindigar.

A cewar Abdulrahman Usman, dakarun runduna ta 1 ta barikin Dukku da ke birnin Kebbi ne suka kai sumamen kan tsaunukan Kogon Damisa da ke Saminaka a Karamar Hukumar Shanga da ke kan iyakar jihar ta Kebbi da makwabciyarta Jihar Neja.

Daraktan tsaron, ya ce yayin sumamen wanda ya gudana da taimakon jami’an sa kai, an yi nasarar kame tarin ‘yan bindiga baya ga ceto mutanen 6 wadanda suka bace tsawon lokaci.

Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike 

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida