Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 20, sun ƙwato litar mai 90,000

Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai samame domin kawo ƙarshen ayyukan masu satar ɗanyen mai.

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 20, sun ƙwato litar mai 90,000

Rundunar Sojin Najeriya, da ke Fatakwal ta lalata haramtattun matatun 20 tare da ƙwato litar man fetur sama da 90,000 da aka sace a yankin Neja Delta.

Daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Disamba, 2024 sojoji sun kuma lalata kwale-kwale guda 21 da ake amfani da su wajen satar mai, tare da kama mutum takwas da ake zargi.

A yayin samamen, an gano manyan tankunan ajiyar mai ɗauke da man da aka sato, da kuma haramtattun kayan aikin tace mai a Jihohin Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, da Delta.

A Ƙaramar Hukumar Asari-Toru, sojoji sun gano babban tankin roba ɗauke da litar mai 37,000 na man sata tare da kama jiragen ruwa guda uku na ɗaukar ɗanyen mai.

Hakazalika, a kogin Imo, rundunar ta lalata haramtattun matatun mai guda bakwai da kuma kwantina guda 122 ɗauke da litar mai sama da 10,000 na man da aka sace.

Rundunar sojin ta yi alƙawarin ci gaba da sanya ido kan masu aikata laifuka.

Ta kuma yi kira ga dakarunta da su ci gaba da ƙoƙari wajen daƙile satar man fetur domin bunƙasa tattalin arziƙin a yankin.