Sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur a Ribas

A gefe guda, dakarun sun kuma da wasu ‘yan ta’adda da dama a Jihar Neja.

Sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur a Ribas

Dakarun Sojin Saman Najeriya, sun lalata wasu haramtattun matatun man fetur guda uku tare da kawar da ‘yan ta’adda a Jihar Ribas.

Darakta hulɗa da jama’a na rundunar, AVM Edward Gabkwet ne, ya sanar da hakan a ranar Lahadi.

Gabkwet, ya bayyana cewar ayyukan masu satar mai na ci gaba da yin ƙamari ta hanyar kafa haramtattun matatar man fetur a jihar

A cewarsa, NAF tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro na ci gaba da inganta fasaha da dabarun yaƙi da masu satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta.

Kazalika, ya ce rundunar ta lalata wasu wurare uku da ake amfani da su wajen satar man fetur ta hanyar amfani da jiragen ruwa.

A gefe guda kuma, ya ce NAF ta yi sanar kawar da wasu ’yan ta’adda a yankin Kuchi-Kapana da ke Jihar Neja.

A cewarsa ayyukan rundunar sun yi tasiri, inda suka ƙwato wa mazauna yankin shanun da suka sace musu, tare da ba su tabbacin ci gaba da ba su tsaro.

Gabkwet, ya bayyana muhimmancin ci gaba da yin haɗin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.

Nahiyar Afirka na da abin da za ta dogara da kanta — Tinubu

Masu dakon man fetur sun ƙara farashi

Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano

EFCC ta kama jami’an Gwamnatin Katsina kan sace tallafin N1.3b