Sojoji sun mammari wanda ya tattaki daga Legas don Buhari saboda ya ki keta dokar hanya

Wasu sojoji uku a cikin motoci biyu da cunkoson ababen hawa ya rutsa da su a kan titi, sun azabtar da Sulaiman Hashim wanda ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja don murnar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sakamakon dogewa da ya yi na tsayawa a kan hannunsa a yayin da suke tursasa wa masu […]

Sojoji sun mammari wanda ya tattaki daga Legas don Buhari saboda ya ki keta dokar hanya
Sojoji sun mammari wanda ya tattaki daga Legas don Buhari saboda ya ki keta dokar hanya

Wasu sojoji uku a cikin motoci biyu da cunkoson ababen hawa ya rutsa da su a kan titi, sun azabtar da Sulaiman Hashim wanda ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja don murnar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sakamakon dogewa da ya yi na tsayawa a kan hannunsa a yayin da suke tursasa wa masu motoci, don sama wa kansu hanyar wucewa daga cinkoson. 

Lamarin wanda ya faru a ranar Litinin da ta gabata a kan titin Olusegun Obasanjo da ke Birnin Tarayya Abuja, ya dada jawo karin cinkoson ababen hawa a kan titin, wanda motoci masu bin layin mai suka haddasa tun daga farko.
Aminiya ta samu labarin cewa sojojin uku sun yi ta marin Sulaiman tare da hankada shi, kafin wadansu daga cikin wadanda suka nemi shiga tsakani, su shaida shi, inda suka ankarar da sojojin game da shi, lamarin da ya sa biyu daga cikinsu wadanda sojan kasa ne suka gudu suka bar sojan ruwa da suke tare.
Wata da lamari ya auku a kan idonta ta da ta nemi a sakaye sunanta, ta bayyana wa wakilinmu cewa, sojan na uku shi ma ya so ya sulale, amma sai jama’a suka rike shi kafin wasu ’yan sanda su taho su tafi da shi zuwa ofishin ’yan sanda na Wuse tare da Sulaiman, inda suka dauki bayanansu a kan al’amarin.
Sulaiman Hashim wanda mammary da sojojin suka yi masa ya sa idanunsa biyu sun bayyanar da digon jini, ya koka kan yadda jikinsa ke yi masa ciwo, inda aka kai shi Asibitin Maitama da ke Abuja da misalin karfe 7:00 na dare a ranar don duba duba lafiyarsa.