Sojoji sun raba magunguna kyauta ga mutum 3000 a Neja
Jami’an sojojin Najeriya sun raba kyautar magunguna a garin Kontagora jihar Neja, a wani shiri da suka kaddamar na kwanaki biyu don tallafawa mazauna yankin. Shirin ya tallafa wa marasa lafiya da suka kai dubu 3 da ya hada mata da yara. A yayin bayar da tallafin an gudanar da gwajin cutar HIV/AIDS da gwajin […]
Jami’an sojojin Najeriya sun raba kyautar magunguna a garin Kontagora jihar Neja, a wani shiri da suka kaddamar na kwanaki biyu don tallafawa mazauna yankin.
Shirin ya tallafa wa marasa lafiya da suka kai dubu 3 da ya hada mata da yara.
A yayin bayar da tallafin an gudanar da gwajin cutar HIV/AIDS da gwajin cututtuka da gawajin ciwon ido tare da bada magani ko gilashi da kuma maganin ciwon hakori. An kuma rabawa marasa lafiyan gidan sauro.
Kwamandan rundunar Sojojin Kontagota Manjo Janar Abubakar Adamu Tarfa ne ya jagoranci shirin.