Sojoji sun ragargaji Boko Haram
Mazauna garin Maiduguri na Jihar Borno sun kadu sakamakon harin mayakan kungiyar Boko Haram da suka nemi kutsawa cikin garin kafin sojoji su fatattake su. Jam’a sun yi ranta a na kare yayin da sojoji ke yi wa mayakan luguden wuta a harin da kungiyar ta kai a kokarinta na shiga barikin sojoji na 333 […]
Mazauna garin Maiduguri na Jihar Borno sun kadu sakamakon harin mayakan kungiyar Boko Haram da suka nemi kutsawa cikin garin kafin sojoji su fatattake su.
Jam’a sun yi ranta a na kare yayin da sojoji ke yi wa mayakan luguden wuta a harin da kungiyar ta kai a kokarinta na shiga barikin sojoji na 333 da ke Maiduri a daren Litinin.
“Sun yi yunkurin shigowa ta Kauyen Gamboyi amma sojoji suka buda musu wuta lamarin da ya sa su tserewa. An magance matsalar kuma babu wanda aka kashe mana”, inji wata majiyar tsaro.
Mazauna Maiduguri sun bayyana kaduwa da jin harbe-harben a lokacin da ‘yan Boko Haram suka bude wuta a unguwannin da ke kusa da barikin sojoji na 333.
Wani dan jarida, Haruna Dauda Biu ya bayyana matukar razana da harin da kuma yananin da ya biyo baya.
“Mun kasa barci sai kusan 1.00 na dare tun daga lokacin da aka fara habe-harben da misalin 11.00 na dare.
“Hankalina ya tashi sosai, na kira wani Janar din soja wanda ya ce min za su magance matsalar”, inji shi.
Wani Mazaunin Maiduguri, Muhammadu Kundiri ya ce fararen hula sun yi ta shiga dazuwa domin neman tsira, yayin da jirgin sama ke ta shawagi na tsawon sa’o’i.