Sojoji sun rutsa da barayin shanu a Zamfara
Sojojin Runduna ta daya da suke aikin kawar da barayin shanu da masu satar mutane a yankin Arewa maso Yamma sun fantsama cikin dazuzzukan da ke Jihar Zamfara a daidai lokacin da ake ruwan sama kamar da baki kwarya a ranar Litinin da ta wuce inda suka samu nasarar kama wadansu daga cikin barayin shanun […]
Sojojin Runduna ta daya da suke aikin kawar da barayin shanu da masu satar mutane a yankin Arewa maso Yamma sun fantsama cikin dazuzzukan da ke Jihar Zamfara a daidai lokacin da ake ruwan sama kamar da baki kwarya a ranar Litinin da ta wuce inda suka samu nasarar kama wadansu daga cikin barayin shanun da ake nema ruwa a jallo.
Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya fadi a wata sanarwa cewa sojojin sun kai hare-hare a dazuzzukan Batara da Ajah da ke kananan hukumomin Birnin Magaji da Gusau, kuma duk da barayin shanun sun gudu, sojoji sun lalata sansanoninsu tare da kwato babura uku da wayoyin hannu biyu.
Sai dai a harin da suka kai dajin Rimawa da ke karamar Hukumar Gusau sun kama biyu daga cikin barayin shanun da ake nema masu suna Aliyu Abubakar da Umar Ibrahim, yayin da a dajin kauyen Bini da ke karamar Hukumar Maru sojojin suka samu nasarar kama wani fitaccen mai hada baki da ’yan fashi da makami da ya addabi jama’a, mai suna Umar dan Bilbili.