Sojoji sun sake kwato shanu daga barayin dabbobi

Sojojin Runduna ta daya da ke Kaduna sun yi bindige wadansu ’yan fashi biyu a kan hanyar Pambeguwa da ke karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna.Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Rundunar Sojin ta daya, Kanar Usman Abdul ta ce sojojin sun kwato mota kirar Toyota Hilud mai lamba ABC 101 HM da bindiga […]

Sojoji sun sake kwato shanu daga barayin dabbobi
Sojoji sun sake kwato shanu daga barayin dabbobi

Sojojin Runduna ta daya da ke Kaduna sun yi bindige wadansu ’yan fashi biyu a kan hanyar Pambeguwa da ke karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Rundunar Sojin ta daya, Kanar Usman Abdul ta ce sojojin sun kwato mota kirar Toyota Hilud mai lamba ABC 101 HM da bindiga mai dauke da harsasai da kuma kudin da suka kai Naira dubu 310, sai kuma wayar salula guda daya.
Sanarwar ta bukaci duk wanda motarsa ta bata ya ziyarci hedikwatarta da ke Kawo domin ya duba.
Har ila yau, a cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce an kafa hadin gwiwar jami’an tsaro mai taken “SHARAR DAJI” a yankin Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya domin karkade miyagu daga yankunan.
A cewar sanarwar, Rundunar Sharar Dajin an kafa ta ce da nufin share miyagun iri da barayin shanu daga cikin dazuzzukan da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Babban Kwamnadan Runduna ta daya, Manjo Janar Adeniyi Oyebade a lokacin da yake ziyarar wuraren da sojojin ke aiki ya yaba wa jami’an tsaron kan kokarinsu na kawar da batagari a cikin al’umma. Ya ce sojojin sun yi nasarar kwato shanu da yawa daga maboyar barayin shanu a Arewa ta Tsakiya inda ya ce kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kawo karshen sace-sacen shanu da fashi da makami a yankin.