Sojoji sun sake maida ‘yan gudun hijira gidajensu a Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta fara maida ‘yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin su na Sabon Gari a karamar hukumar Dambuwa a jihar Borno. Sabon gari ya kai nisan kilomita 34 daga cikin Dambuwa, yayin  da kuma ya kai nisan kilomita 100 daga Dambuwa zuwa garin Biu. Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole […]

Sojoji sun sake maida ‘yan gudun hijira gidajensu a Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta fara maida ‘yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin su na Sabon Gari a karamar hukumar Dambuwa a jihar Borno.

Sabon gari ya kai nisan kilomita 34 daga cikin Dambuwa, yayin  da kuma ya kai nisan kilomita 100 daga Dambuwa zuwa garin Biu.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole , Manjo Janar Benson Akinroluyo ne ya sanarwa manema labarai hakan a yau. Kwamandan ya tabbatar cewa, maida ‘yan gudun hijirar zuwa gidajensu na daya daga cikin ayyukan rudunar a yankin.