Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turji a Zamfara
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara.
![Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turji a Zamfara Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turji a Zamfara](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/122582288_belloturjizamfarasuspectedbanditkingpinbelloturjiprofile.jpg.webp)
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara.
Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro.
Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato.
Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska.
- ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai
- ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano
Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan da ke ƙauyen Dakai.
Sojojin sun kona sansanin tare da ceto mata da ƙananan yara da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
Sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 da bama-bamai da gurneti da ’yan bindigar suka tsere suka bari.