Sojoji sun tarwatsa maboyar Boko Haram a Borno

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) a shirinsu na farautar mayakan Boko Haram, sun tarwatsa maboyar sansanin ‘yan kungiyar da wasu motocinsu a unguwar Tumbun Sale a Arewacin jihar Borno. Kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Iya Kwamando Ibikunle Daramola ne ya fitar da sanarwar a yau Alhamis. Ya ce, rundunar sojin ta gano motocin da ‘yan […]

Sojoji sun tarwatsa maboyar Boko Haram a Borno

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) a shirinsu na farautar mayakan Boko Haram, sun tarwatsa maboyar sansanin ‘yan kungiyar da wasu motocinsu a unguwar Tumbun Sale a Arewacin jihar Borno.

Kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Iya Kwamando Ibikunle Daramola ne ya fitar da sanarwar a yau Alhamis. Ya ce, rundunar sojin ta gano motocin da ‘yan Boko Haram ke amfani da su wajen kai hare-hare da kuma kakin sojoji da aka boye a sansanin.

Daramola ya ce, jirgin sojin sama mai saukar angulu ne ya taimaka wajen gano maboyar Boko Haram.