Sojoji sun tarwatsa sansanin ’yan bindiga da kuɓutar da wasu
Sansanin masu garkuwa da mutanen da aka tarwatsa yana unguwar Punkun a Fikyu, Karamar hukumar Ussa ta jihar Taraba.
Sojojin Najeriya da ke karkashin Operation Whirl Stoke a Jihar Taraba sun yi nasarar fatattakar masu garkuwa da mutane tare da kuɓutar da wasu da dama da aka yi garkuwa da su.
Mukaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Oni Olubodunde, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
- An Kama ’Yar Sanda Kan Satar Yara Daga Sakkwato zuwa Abuja
- Mai shago ya sace yarinya ya boye ta a firinji a Kaduna
Ya ce, sansanin masu garkuwa da mutanen da aka tarwatsa yana unguwar Punkun a Fikyu, Karamar Hukumar Ussa ta jihar.
Olubodunde ya ci gaba da cewa, sojojin da ke aikin leken asiri sun yi nasarar fatattakar ’yan bindigar tare da tarwatsa sansaninsu da kuma kwato makamai da dama.
“Sojojin da aka tura a unguwar Kufai Amadu da Kasuwan Haske sun tarwatsa maɓoyar ’yan bindigar a kauyen Vingir na Karamar hukumar Katsina-Ala, a jihar Binuwai,” inji shi.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa, an kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Dogo Manu da wayoyin hannu biyu da kuma kudi Naira 40,000.
Oni ya kara da cewa, ana ci gaba da bincike a sansanin masu garkuwa da mutane, inda aka samu nasarar kwato bindiga kirar AK 47 guda ɗaya.