Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram a Ngwuri Gana

Rundunar sojin saman Najeriya NAF ta ce, jirgin yakin saman sojoji a shirinsu na Operation Lafiya Dole da suka yi ranar 5 ga Nuwamba 2018 sun tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram tare da raunata maharan a Ngwuri Gana da ke Borno. Rundanar ta ce, sansanin wata moboya ce da ‘yan Boko Haram ke shirya kaiwa […]

Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram a Ngwuri Gana

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Rundunar sojin saman Najeriya NAF ta ce, jirgin yakin saman sojoji a shirinsu na Operation Lafiya Dole da suka yi ranar 5 ga Nuwamba 2018 sun tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram tare da raunata maharan a Ngwuri Gana da ke Borno.

Rundanar ta ce, sansanin wata moboya ce da ‘yan Boko Haram ke shirya kaiwa jama’a hari a yankunan da ke garin Kumshe.

Kakakin rundunar Eya Kwamanda Ibikunle Daramola, ya tabbatar da aukuwar hakan ya kara da  cewa, sansanin na daya daga cikin maboyar Boko Haram.