Sojoji sun ‘tozarta’ Tambuwal
A ranar Litinin wasu sojoji sun ‘tozarta’ Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Waziri Tambuwal a Kaduna,inda suka nace sai sun binciki motarsa kafin su bar shi ya shiga wurin wani taro da aka shirya zai zama babban mai jawabi.Lamarin ya faru ne a otel din 17th Hotel Kaduna wurin da aka gudanar da babban taro kan […]
A ranar Litinin wasu sojoji sun ‘tozarta’ Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Waziri Tambuwal a Kaduna,inda suka nace sai sun binciki motarsa kafin su bar shi ya shiga wurin wani taro da aka shirya zai zama babban mai jawabi.
Lamarin ya faru ne a otel din 17th Hotel Kaduna wurin da aka gudanar da babban taro kan tsaro da ci gaban kalubale da ke shafar makiyaya a yammaci da tsakiyar Afirka.
Ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro ne ya shirya taron mai taken: “Gudunmawar makiyaya wajen dakile hare-hare da rikice-rikice don inganta tsaron kasa.”
Tambuwal, ya isa wurin taron ne da misalin karfe 9:16 na safe, amma sojojin da ke tsaron kofar shiga suka ce ba za a bar ayarinsa ya shiga ba, wani ganau ya ce, hatta lokacin da motar shugaban ta zo, sai sojojin suka ce ta tsaya a bincike ta ko akwai bam, kuma daya daga cikinsu ya bukaci a saukar da gilashin motar.
Majiyar ta ce bayanin da jami’an tsaron Tambuwal suka yi ya bi ta bayan kunnen sojojin wadanda suka nace sai sun binciki motar. “Lokacin da cin fuskar ya yi yawa, sai shugaban majalisar ya fito daga motar ya taka a kafa zuwa cikin otel din,” inji majiyar.
Majiyar ta ce, ta ji mamaki lokacin da wasu gwamnoni suka zo daga baya amma ba wanda ya yi yunkurin tsayar da motocinsu don bincikarsu.
Kakakin Tambuwal, Malam Imam Imam ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya shawarci sojoji su rika martaba ofishin shugaban majalisar.
Ya ce, “A matsayinsa na mutum na hudu, shugaban majalisar ya cancanci girmamawa daga daukacin ’yan Najeriya. Abin da ya faru abin takaic ne, wajibi ne mu girmama ofishin shugaban, kuma motarsa ta aiki alama ce ta wannan ofishi.”
Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya aika da takardar neman gafara ga Aminu Tambuwal kana bin da sojojin suka yi masa.
Wakilinmu ya ga kwafen wasikar da Sambo Dasuki ya nemi garafar shugaban majalisar.
Dama mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro ya ba da umarnin a binciki lamarin.