Sojoji sun yi aikin gyaran hanya a Abeokuta
Sojojin Bataliya ta 35 na Atilare da ke Barikin Alamala a Abeokuta a Jihar Ogun sun yi aikin gyaran hanyar Randa wacce da ta dade tana ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya. Da yake kaddamar da aikin gyaran hanyar a daura da shataletalen Randa da ke daura da Kasuwar Shanu ta Randa a Abeokuta, […]
Sojojin Bataliya ta 35 na Atilare da ke Barikin Alamala a Abeokuta a Jihar Ogun sun yi aikin gyaran hanyar Randa wacce da ta dade tana ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya.
Da yake kaddamar da aikin gyaran hanyar a daura da shataletalen Randa da ke daura da Kasuwar Shanu ta Randa a Abeokuta, Kwamandan Runduna ta 81 ta sojin Najeriya da ke Legas Manjo Janar Olu Irefin ya ce, aikin bangare ne na shirin Murmushin Kada Kashi na 4 da aka kaddamar a Jihar Ogun. Ya ce al’ummar jihar masu bin doka da oda ba su da haufi domin shirin an shirya shi ne domin maganin batagari masu miyagun ayyukan da suka shafi fasa bututun man fetur da masu garkuwa da mutane da sauransu. Ya ce rundunar sojin na aiki tare da sauran jami’an tsaro don haka za ta mika wadanda ake zargin ga hukumar da ta dace domin zurfafa bincike. “Don haka muke aiki da ’yan sanda da jami’an tsaro na Sibil Difens, duk wanda muka kama za mu mika shi gare su gwargwadon laifin da ya aikata,” inji shi.
Ya ce, a daya bangaren rundunar sojin ta kaddamar da ayyukan more rayuwa ga al’ummar yankin domin su amfana. Ya ce gyaran hanyar zai taimaka wa shige da ficen jama’a cikin sauki tare da inganta tsaro.
Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin jama’ar yankin inda suka bayyana farin cikinsu kan gyaran hanyar da bataliyar sojin Atilare ta 35 ta yi a karkashin jagorancin Kwamandanta Birgediya Janar. E.J. Amadasun, inda suka ce gyaran hanyar tamkar share musu hawaye ne ganin yadda rashin gyaran hanyar ya gurgurta al’amura a yankin.
Hanyar Randa babbar hanya ce, mallakar Gwamnatin Tarayya da ke da muhimmanci domin ta hade da jihohin Ogun da Oyo ta bangaren Iseyin ta kuma hade jihar da Legas ta yankin Itoshi kana ta hade Najeriya da Jamhuriyyar Benin, sannan hanya ce da ake amfani da ita zuwa manyan kasuwanni da suka hadar da Kasuwar Shanu ta Randa da Olodo da Jami’ar Crescent da sauran manyan makarantu a yankin.