Sojoji sun yi bayani kan fadowar jirginsu a Kaduna

Jirgi mara matuki ne ya faɗo yayin aikin sintirin samar da tsaro

Sojoji sun yi bayani kan fadowar jirginsu a Kaduna

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar da fadowar jirginta a safiyar Litinin.

Kakakin rundunar, Edward Gabwet, ya ce jirgin ya fado ne sakamakon matsalar da ya samu a yayin gudanar da aikin sintiri,

Gabwet ya ce hakan ya faru ne jim kadan bayan tashin jirgin daga sansanin sojoji zuwa yankin Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Amma ya ce duk da abin da ya faru, hakan ba zai kawo tsaiko ga aikin da rundunar soji ke ci gaba yi na samar da tsaro ba.

Ya kuma bayyana cewa jirgi mara matuki ne abin ya ritsa da shi don haka babu asarar rai.

Don haka ya ce rahoton da ke yawo cewa jirgin soji mai saukar ungulu ne abin ya rutsa da shi ba daidai ba ne.

A cewarsa ya nemi ’yan jarida su rika tantance duk abin da ya faru da daga hukumomin da ya kamata kafin su wallafa.

Aminiya ta ruwaito wani mazaunin kauyen Tami da ya bi shaida mata cewa jirgin ya fado ne da misalin karfe 5 na asuba.

Shaidan ya kuma bayyana cewa matukin jirgin ya fito daga cikim tarkacen kafin daga bisani sojoji su iso wurin domin gudanar da bincike.

Kafin wallafa rahotonmu na farko wakiliyarmu ta kira kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya na Jihar Kaduna, amma ya yi ta katse kiran.

Amma Gabwet ya ce jirgi mara matuki ne ya fado ya kuma tabbatar da abin da shaidan ya fada cewa jami’an rundunar sun wurin domin gudanar da bincike.