Sojoji sun yi dirar mikiya a kasuwa bayan dukan abokin aikinsu a Abuja
An ji wani a kasuwar yana kururuwar cewa, “Wannan yaƙin duniya na biyu ne.”
Sojoji sun yi dirar mikiya a kasuwar Banex da ke Abuja, babban birnin ƙasar bayan harin da aka kai wa wasu abokan aikinsu.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin na zuwa ne bayan wasu ɓata-gari sun afka wa akalla sojoji biyu a kasuwar da ta shahara da sayar da na’urorin lantarki da wayoyin hannu.
- ‘Gwamnatin Tarayya ta mayar da Arewa maso Gabas saniyar ware’
- Kirifto DA ‘Mining’ A Tsakanin Matasan Arewa!
Ɓata-garin waɗanda suka rabu kashi-kashi har uku sun riƙa mari da dukan sojojin da ke sanye da kaki.
Bayanai sun ce wannan lamari ya sanya wasu ’yan kasuwar suka rufe shaguna suka haƙura da ƙarasa cin kasuwar wannan rana kuma suka tsere gida sakamakon fargabar abin da zai je ya komo.
Sai dai sa’o’i bayan faruwar lamarin, sojoji ɗauke da makamai suka mamaye kasuwar, inda mutane suka riƙa gudun neman mafaka.
A cikin wani bidiyon da aka naɗo faruwar lamarin, an ji wani yana kururuwar cewa, “Wannan yaƙin duniya na biyu ne.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa sojoji sun jibge motocin dama a wurare daban-daban, sai dai babu tabbas ko an kama mutane a lokacin haɗa wannan rahoto.
Kawo yanzu dai babu musabbabin faruwar lamarin, sai dai wani ɗan kasuwa ya shaida wa Aminiya cewa an kai wa sojojin hari ne bayan an samu rashin jituwa da wasu mutane a kasuwar.
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ya ci tura a yayin da ba ta amsa kira da wakilinmu ya yi mata ba.