Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
Sojojin sun soke zaɓukan ‘yan majalisa da na shugaban ƙasa da aka gudanar.
Sojoji a Guinea-Bissau sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar baki ɗaya.
Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.
- ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
- Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
Wannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.
A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.
Cikakken rahoto na tafe…