Sojoji sun yi kawanya ga ’yan Boko Haram a dajin Sambisa – Buratai

Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Buratai, ya fadi a shekaranjiya Laraba cewa sojojin kasa sun yi kawanya wa mayakan Boko Haram ta yadda ba su iya shiga ko fita daga dajin Sambisa.Janar Buratai ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya lura da yadda aka tura […]

Sojoji sun yi kawanya ga ’yan Boko Haram a dajin Sambisa – Buratai
Sojoji sun yi kawanya ga ’yan Boko Haram a dajin Sambisa – Buratai

Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Buratai, ya fadi a shekaranjiya Laraba cewa sojojin kasa sun yi kawanya wa mayakan Boko Haram ta yadda ba su iya shiga ko fita daga dajin Sambisa.
Janar Buratai ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya lura da yadda aka tura sojojin garin Banki da ke iyakar Najeriya da Chadi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Janar Buratai yana cewa Shirin Murkushewa da sojojin suka kaddamar yana samun nasara, inda sojojin kasa suke ci gaba da rusa sauran maboyar Boko Haram a dajin Sambisa.
 “Sojojin suna taka rawar gani; suna haduwa da wasu matsaloli wajen fafatawa da ’yan ta’addan da ke fagen daga, amma ana magance hakan. Sojojin suna kawanya don hana ’yan ta’addan shiga ko fita daga yankin. Kuma na zo nan ne domin in ga sojojin kasa da yadda suke gudanar da aiki, aiki na tafiya daidai, amma ana can ana fama yanzu haka a cikin dajin Sambisa,” inji shi.
Janar Buratai ya ce ajiye sojojin kasa a mahadar Banki yana da muhimmanci ga aikin soja domin a hana ’yan ta’addan= shigowa kasar nan ta kasar Kamaru ko Chadi.
“Muna tare da Babban Hafsan Tsaro da Babban Hafsan Sojin Sama a Maiduguri, inda kwamandan hedkwatar yaki da ta’addancin ya yi mana bayani kan shirin kawar da ’yan ta’addan. Wannan mahada ta Banki babbar hanya ce da ta hada Arewa da Kudu, kuma ta yi iyaka da Kamaru; kuma tana shiga kasar Chadi. Babbar hanya ce da Boko Haram suke amfani da ita a tsakanin dajin Sambisa da arewacin kasar nan har zuwa Tafkin Chadi. Don haka muhimmin wuri da zai kasance wajen tsara dabaru da gudanar da ayyukan da muke yi a wannan yanki,” inji Janar Buratai.
Ya ce sojojin kasa da taimakon jiragen yaki na sojin sama za su ci gaba da kai farmaki a cikin dajin har sai an murkushe ’yan ta’addan.
A ranar Litinin ne Babban Hafsan Tsaro Laftana Janar Gabriel Olonisakin da Laftana Janar Tukur Buratai da takwaransa na sojin sama Iya marshal Abubakar Siddikue suka gana a asirce don nazarin abin da yake gudana a dajin na Sambisa, wanda aka faro ranar 27 ga Afrilu.