Sojoji sun yi kuskuren kashe fararen hula 13 a Neja
An kai harin ne kan maɓoyar ’yan ta’adda a Kusasu, amma cikin rashin sa’a bam ɗin da aka jefa ya kashe mutum 13.
Wasu hare-haren sama da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a ƙarshen mako a Jihar Neja sun yi sanadin mutuwar fararen hula 13, kamar yadda majiyoyin yankin suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, yayin da sojoji suka ce harin ya kashe ’yan bindiga sama da 70.
An kai hare-haren ne a ƙaramar hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, yankin da kwanakin nan ya zama mafakar wasu mayaƙan Boko Haram da kuma ƙungiyoyin ’yan bindiga masu kai hare-hare kan ƙauyuka da ƙaƙaba haraji a wuraren da gwamnati ba ta da cikakken iko.
- Sahun farko na maniyyatan Sakkwato sun sauka a Madina
- Maniyyaciyar Taraba ta rasu a hanyar zuwa Saudiyya
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe fararen hula a garin Kusasu, duk da cewa ta ce za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen.
Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro, Isyaku Bawa, ya shaida wa AFP cewa harin saman da aka kai ranar Lahadi ya afka wa mutane bisa kuskure.
“An kai harin ne kan maɓoyar ’yan ta’adda a Kusasu, amma cikin rashin sa’a bam ɗin ya faɗa kan mutane kuma an yi asarar rayuka na mutum 13,” in ji shi.
Sai dai jaddada cewa harin ya auku ne bisa kuskure domin ba da gangan aka yi shi ba, yana mai jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu.
Wani mazaunin yankin da ya rasa ’yarsa da wasu ’yan uwansa biyu ya ce sun binne gawarwaki 13 bayan harin.
“An kai waɗanda suka jikkata asibiti. ’Yata da ’yar babban yayana da kuma yayata duk sun mutu,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin mai suna John Ezra ya ce gidajensu ne aka jefa wa bama-bamai duk da cewa ba su kusa da maboyar ’yan ta’addar, inda shi ma ya tabbatar da mutuwar mutum 13.
Sai dai a wata sanarwa da rundunar soji ta fitar a ƙarshen mako, ta ce ta kai hare-hare a wurare daban-daban da suka haɗa da ƙauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da Kuduru.
Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce kimanin ’yan bindiga 70 ne suka mutu a Kusasu.
Ya kuma ce dukkan al’ummomin fararen hula da ke yankin sun riga sun ƙaurace wa matsugunansu kafin kai harin.
“Ana zargin cewa babu fararen hula a wuraren da aka kai hare-haren,” in ji shi.
Sai dai ya ce an umarci rundunonin da abin ya shafa su binciki zargin mutuwar fararen hula idan har hakan ta auku.
Kawo yanzu dai an kashe ɗaruruwan fararen hula cikin tsawon shekaru 17 da Najeriya ta shafe tana yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.
Ana iya tuna cewa, a ranar Lahadin da gabata ce, wani ɗan sa-kai ya shaida wa AFP cewa ana fargabar mutuwar ɗimbin masunta sakamakon hare-haren da sojojin Chadi suke ci gaba da kai wa a Tafkin Chadi tun daga ranar Juma’a.
Tafkin Chadi, wanda ya haɗa Najeriya da Chadi, na zama mafakar mayaƙan Boko Haram da kuma ISWAP.
A watan Afrilu ma, rundunar sojin Najeriya ta kai hari kan wata kasuwa a Jilli da ke iyakar jihohin Yobe da Borno, inda aka kashe aƙalla mutum 56, yawancinsu fararen hula.
Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, sai dai har yanzu ba a fitar da sakamakonsa ba.