Sojoji sun yi nasarar hallaka ’yan ta’adda 11 a Yobe
Sojojin sun yi karon-batta da wasu ‘yan bindigar a yankin Wajiroko Sabongari.
Dakarun rundunar tsaro ta Operation Haɗin Kai sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 11 a wani samame na musamman a iyakar Jihar Yobe.
Kakakin rundunar ta musamman, Laftanar- Kanar Sani Uba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wannan Larabar.
- Ƙyanda ta kashe fiye da yara 220 a Bangladesh
- Sheikh Adam ya jagoranci limamai a Yobe wajen yi wa Najeriya addu’a
Ya bayyana cewa sun hallaka ‘yan ta’adda ne bayan samame da suka kai maɓoyarsu da ke Mar, Subdu, Yaro Lawanti da Yaro Shuwari da sauran wuraren da ke kewaye da dajin Bulabulin.
Uba ya ce jami’an tsaron sama sun taimaka ƙwarai wajen bayar da bayanan sirri da sanya ido da kuma shirya yadda za a far musu tare da jami’an kan tudu.
“A yankin dajin Bulabulin, jami’ai sun gamu da ‘yan ta’adda ne a ƙauyen Malam Shiri, a nan suka buɗe musu wuta. An samu nasarar hallaka mutum 11 a cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an sun lalata maɓoyar ‘yan ta’addan inda suka samu bindiga ƙirar AK47 guda tara, da bindiga mai jigida guda uku, da babura biyar, da kayayyakin haɗa bam.
A wani samamen mai kama da wannan, sojojin sun yi karon-batta da wasu ‘yan bindigar a yankin Wajiroko Sabongari, inda suka yi ɗauki-ba-daɗi.
Uba ya ce sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda aƙalla guda bakwai, da raunata da dama da ba a tantance adadinsu ba.
Rundunar ta samu nasarar ƙwato muggan makamai da bindigogi iri-iri da harsasai.
Kakakin ya ce rundunar tsaron Najeriya ta kuma kai harin sama a matsugunnan ‘yan ta’adda dama kuma an lalata garkuwarsu.
Uba ya ce yanzu haka rundunar ta haɗa gwiwa da jami’an sa-kai, inda take kai sumame a yankunan Forfor, Multe, da Wajiroko, domin bin sahun ‘yan bindigar da suka tsere.