Sojoji sun yi wa magoya bayan APC bulala a gaban iyalansu
’Ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa da suka hada da Alhaji Garba Hannun Giwa da Abdullahi Ojo Gumel da takarar sanata a jam’iyyar da tsohon shugaban kungiyar ’Yan Jarida ta kasa (NUJ) Alhaji Sani Muhammed Zoro sun nuna damuwa kan matakin da shugabannin kananan hukumomin Gumel da Gagarawa suka dauka na amfani da sojoji da […]
’Ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa da suka hada da Alhaji Garba Hannun Giwa da Abdullahi Ojo Gumel da takarar sanata a jam’iyyar da tsohon shugaban kungiyar ’Yan Jarida ta kasa (NUJ) Alhaji Sani Muhammed Zoro sun nuna damuwa kan matakin da shugabannin kananan hukumomin Gumel da Gagarawa suka dauka na amfani da sojoji da ’yan dabar siyasa suka ci mutuncin magoya bayan jam’iyyar a gaban iyalansu a makon jiya.
Alhaji Sani Zoro wanda jagoranci ’ya’yan jam’iyyar suka gana da manema labarai a cibiyar ’yan jarida da ke Dutse, ya kuma zargi shugaban yankin Gagarawa da takwaransa na Gumel Alhaji Ala Gumel da jagorantar sojojin Operation Salama zuwa wuraren zaman jama’a da gidajen ’yan jam’iyarsu suna sa su tsallen kwado da yi musu bulala a gaban matansu da ’ya’yansu.
Alhaji Sani Zoro ya ce ba za su amince da irin wannan cin mutuncin da sojojin suka yi wa magoya bayansu ba domin an ke ta musu haddi kuma hakan ya saba wa shari’a da zaman da suka yi da kwamishinan ’yan sanda.
Ya yi zargin cewa Gwamna Sule Lamido ne ya sa suka afka wa jama’a domin shi ne ya ce
su afka wa ’ya’yan APC a ko’ina suke a wajen yawan kamfe din tan takararsu na PDP a kauyen Buji.
A wani labarin wasu matasa dauke da ake zaton magoya bayan Jam’iyyar PDP ne dauke da makamai sun kai hari kauyen Giwa da ke karamar Hukumar Birnin Kudu inda suka kone ofishin Jam’iyyar APC suka raunata matasa biyu tare da kone gidaje tara a garin Giwa da kauyen Bakatima.
Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Malam Bala Giwa ya shaida wa Aminiya da ta ziyarci yankin cewa suna zaune da misalin karfe 4:00 na yamma kawai sai suka ga jerin gwanon motocin PDP suna shigowa garin dauke da miyagun makamai suna zage-zage suna cewa babu APC ba kayanta karyar Badaru.
Ya ce sai kawai matasan suka fara rushe musu rumfunan jam’iyyarsu ta APC suka afka musu daga baya inda mutane da dama ba su yi sallar Magariba da Isha a cikin garin ba a ranar Lahadin da ta gabata.
Sai dai dan takarar Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Ali Tukur Gantsa ya ce abin da ya sani sun shiga kauyukan Jangargari da Wurno da Giwa yada manufar siyasa kuma ba su samu labarin an yi wa wani rauni ba balantana a ce an kona gidajan jama’a. Ya ce ’yan APC ne su kama kona musu ofishin jam’iyya da motarsu suka farfasa musu motoci.
Shugaban Hukumar sibil defens ta Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Gidado Fari ya ce gaskiya ne an yi fada a tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu an kuma kone kayan abinci da gidajen jama’a, amma har zuwa lokacin ba su kama kowa ba, sai dai suna bincike a kan lamarin.