Sojoji sun yi wa masu shirin zanga-zanga kashedi

Sojojin Najeriya sun gargadi masu shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa su shiga hankalinsu

Sojoji sun yi wa masu shirin zanga-zanga kashedi

Sojoji

Rundunar Tsaron Najeriya ta gargadi masu shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya ta ce sojoji ba za su kyale su su tayar da fitina ba.

Hedikwatar Tsaron ta yi gargadin cewa sojoji ba za su zura ido ga a yi kone-kone da dangoginsu na karya doka da oda da sunan zanga-zangar ba.

Dubban ’yan Najeriya musamman matasa sun ayyana 1 ga watan Agusta da ke a matsayin ranar fara zanga-zangar gama gari ta tsawon kwanaki 10 a fadin kasar kan tsadar rayuwa da ta addabe su.

Masu zanga-zangar, mai taken kawo karshe mummunan shugabanci  — #EndBadGovernace — sun nuna damuwarsa kan tsananin yunwa da hauhawan farashin kayan masarufi fiye da kima da ake ci gaba da fama da su a kasar.

Amma da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, Daraktan yada labaran Hedikwatar Tsaron, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojoji ba za su zuba ido Najeriya ta fada a cikin yanayin rashin doka da oda ba.

Manjo-Janar Edward Buba ya ce sojoji sun bankado shirin wasu miyagu na amfani da zanga-zangar domin kawo tashin hankali ta hanyar kai hare-hare kan dukiyoyin al’umma.

“Duk da cewa yan kasa na da yancin su gudanar da zanga-zangar lumana, amma ba su da yancin haddas karya doka ad kuma ta’addanci.”

“Abu mai sauki ne a fahimci cewa zanga-zangar da ke tafe za ta bi sahun wadda ake gudanarwa ce a kasar Kenya, wadda ita ma ta tashin hankali ce, kuma har yanzu ba a shawo kanta ba.”

Buba ya kara da cewa, “Soji ba za su nade hannu suka kasa ta koma babu bin doka da oda ba.

“Dalili kuwa shi ne mun ga irin illa da barnar da rashin bin doka suka yi a kasashen da muka gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, muamman a lokacin rundunar ECOMOG  ta kungiyar kasashen ECOWAS.”

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe