Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Gambiya
Shugaba Adama Barrow ya ce an cafke wasu sojoji hudu da ake zargin su da hannu a yunkurin juyin mulkin na ranar Talata
Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow
Gwamnatin Gambiya ta sanar cewa ta yi nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki da sojojin kasar suka yi.
Shugaban kasar, Adama Barrow ya sanar a ranar Laraba cewa an cafke wasu sojoji hudu da ake zargin su da hannu a yunkurin juyin mulkin na ranar Talata.
- Jarirai 200 aka haifa a sansanin ’yan gudun hijirar Binuwai —NEMA
- Jami’an tsaro sun ragargaji IPOB a Ebonyi da Enugu
“Mun samu bayanan sirri cewa sojoji na kitsa juyin mulki don barar da gwamnatin Dimokradiyya a Gambia a jiya (Talata), amma mun samu nasarar kama sojoji hudu da ke da alaka da hakan.
“Yanzu haka suna hannun rundunar tsaro kuma mun sa a kamo sauran wasu uku da su ma muke zargin da hannunsu a lamarin”, in ji Shugaba Adama Barrow.
Duk da cewa babu tabbacin wadanda suka shirya juyin mulkin, bayanan da gwamnatin ta fitar na nuna cewa an samu zirga-zirgar sojoji a kewayen fadar gwamnatin kasar a ranar Talatar, da kuma yaduwar rade-raden yiwuwar aukuwar juyin mulki a daren ranar.