Sojoji ta fara binciken harin bam a Kasuwar Jilli

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 56, mafi yawansu ’yan kasuwa, ake zargin sun rasa rayukansu, yayin da wasu 14 ke jinya a asibiti

Sojoji ta fara binciken harin bam a Kasuwar Jilli

Sojin Saman Najeriya

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tura tawagar bincike zuwa kasuwar mako-mako ta Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe, bayan rahoton aukuwar harin bam da ya shafi fararen hula.

Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike nan take kan lamarin, inda ya ce rundunar tana ɗaukar duk wani rahoton da ya shafi fararen hula da muhimmanci da tausayi.

Mai magana da yawun rundunar, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan cikin sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, inda ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gano hakikanin lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 56, mafi yawansu ’yan kasuwa, ake zargin sun rasa rayukansu, yayin da wasu 14 ke jinya a asibiti sakamakon harin da ya auka a kasuwar.

Ejodame ya ce, “Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta lura da rahotannin da ke cewa harin da aka kai ranar Asabar 11 ga Afrilu, 2026, ya rutsa da kasuwar Jilli, inda ake zargin ya jawo mutuwar fararen hula.

“Rundunar tana ɗaukar irin waɗannan rahotanni da muhimmanci, domin kare rayukan al’umma na daga cikin ginshiƙan ayyukan NAF.”

Sanarwar ta ƙara da cewa an kafa kwamitin bincike na musamman (CHAI-Cell) domin gudanar da bincike a wurin da lamarin ya faru.

NAF ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare tsaron ƙasa tare da kiyaye rayukan al’umma, tana mai kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yada jita-jita har sai an kammala bincike.