Sojoji za su kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa kafin mika wa Buhari mulki – Dasuki

Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki ya ce sojojin Najeriya za su kakkabe mayakan Boko Haram daga dajin Sambisa kafin Shugaba Goodluck Jonathan ya mika mulki nan da kasa da wata biyu. A ranar 29 ga Mayu mai zuwa ne Shugaba Jonathan zai mika mulki ga Janar Muhammadu Buhari wanda ya kayar da […]

Sojoji za su kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa kafin mika wa Buhari mulki – Dasuki
Sojoji za su kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa kafin mika wa Buhari mulki – Dasuki

Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki ya ce sojojin Najeriya za su kakkabe mayakan Boko Haram daga dajin Sambisa kafin Shugaba Goodluck Jonathan ya mika mulki nan da kasa da wata biyu.

A ranar 29 ga Mayu mai zuwa ne Shugaba Jonathan zai mika mulki ga Janar Muhammadu Buhari wanda ya kayar da shi a zaben 28 ga Maris da ya gabata.
Bayan caccakar sojojin da aka yi na kasa magance hare-haren Boko Haram, a ’yan makonnin nan sojojin sun kwato wasu garuruwa da mayakan Boko Haram suke rike da su, inda suka fatattaki ’yan Boko Haram daga garuruwan Baga da Bama da Gwoza.
Sambo Dasuki, ya shaida wa kafar labarai ta PRNigeria, da ke rarraba takardun sanarwar hukumomin Najeriya cewa, dajin Sambisa da shi ne mafi muhimmanci da Boko Haram ke rike da shi, kamata ya yi a ce tuni an kwato shi, to amma saboda rashin kyawun yanayi a yanki ya hana yiwuwar haka. Ya ce sojoji sun nazarci yanki kuma suna shirye don shiga cikinsa.
“Yanzu haka, an lalata daukacin sansanonin Boko Haram baya ga dajin Sambisa. Kuma ana sa ido kan duk motsin ’yan ta’addan, kuma ana daukar dukkan matakai tare da lura sosai domin kakkabe matsuguni na karshe da ’yan ta’addan ke zaune,” inji Dasuki.
Game da ’yan matan Chibok sama da 200 da ’yan Boko Haram suka sace shekara guda da ta gabata, Kanar Sambo Dasuki ya ce Gwamnatin Tarayya tana kara kokarin don tabbatar da an ceto su.
Ya ce, damuwar gwamnati da ta kowane dan Najeriya ita ce a lafiyar ’yan matan, inda ya bukaci ‘Najeriya su kara hakuri a daidai lokacin da sojoji ke kokarin kakkabe ’yan ta’addan.
Sai ya yaba wa Shugaba Jonathan kan amincewa da shan kaye da ya yi a zaben Shugaban kasa, inda ya ce wannan dattako da ya nuna ya ceto hukumomin tsaro da ita kanta kasar daga shiga halin rudani kuma ya tabbatar da bin doka da oda tare da dakile tashin hankali da zai iya aukuwa daga zanga-zanga.