Sojoji za su sayo jirage 50 domin yaƙi da ta’addanci a Arewa

Air Marshal Hassan ya ce Nijeriya na sa ran karɓar jiragen ya zuwa shekara mai zuwa.

Sojoji za su sayo jirage 50 domin yaƙi da ta’addanci a Arewa

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce za ta sayo sabbin jiragen sama 50 domin ƙara ƙarfinta na yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa masu yamma na kasar.

Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu sabbin sansanonin soji masu ɗauke da wuraren ajiyar jiragen sama biyu a Jihar Katsina.

Air Marshal Hassan ya ce jiragen da za a sayo za su haɗa da masu saukar angulu 12 samfurin AH-1, da jiragen yaƙin soji 24 kirar M-346, da wasu jiragen komai da ruwanka 12 ƙirar AW-109, da kuma jirage 2 na jigilar sojoji.

Babban hafsan bai bayyana adadin kuɗin da za a kashe wajen sayo jiragen ba, da kuma wanda zai kawo jiragen, sai dai ya ce Nijeriya na sa ran karɓar jiragen ya zuwa shekara mai zuwa.

Abubakar ya ce za a yi amfani da jiragen ne wajen kai hari kan ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a jihohin arewa maso yamma da tsakiyar kasar a ’yan shekarun nan.

Sanarwar ta Abubakar ta zo ne bayan wata sanarwa da hukumomin jihar Kaduna suka bayar a ranar Talata, ta hadin gwiwa da rundunar soji domin shirya wurare 3 na fagen dagar yaki da ‘yan ta da kayar baya a jihar, a cewar gwamnan jihar ta Kaduna Uba Sani.

Ya ce “mun yi matsaya da rundunar soji domin kafa sansanonin aiki a kudancin Kaduna, da wani a yankin Giwa da Birnin Gwari, Kuma ana nan ana kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata.

Rundunar sojin saman Najeriya ta fuskanci kakkausan suka a watan Disamban da ya gabata, bayan kashe mutane sama da 80 a wani harin jirgin sama a jihar Kaduna da aka auna gungun ‘yan bindiga. Wasu da dama kuma sun sami raunuka.

Hukumomin Najeriyar sun yi alkawarin kara yin taka-tsantsan domin kaucewa sake aukuwar irin wannan.