Sojojin Nijar sun nada sabon Fira Minista
Sabon Fira Ministan da sojojin suka nada shi ne Ali Mahaman Lamine Zeine, tsohon Ministan Kudi da Tattalin Arzikin kasar.
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta nada ma’aikacin Bankin Raya Afirka a matsayin sabon Fira Ministan kasar, mako biyu bayan sun kifar da Gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.
Sabon Fira Ministan shi ne Ali Mahaman Lamine Zeine, tsohon Ministan Kudi da Tattalin Arziki n a zamanin tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja, wanda aka yi wa juyin mulki a 2010.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Yi Rayuwar Abuja Cikin Sauƙi
- ECOWAS za ta yi sabon taro kan juyin mulkin soji a Nijar
Kakakin gwamnatin sojin da ya sanar da nadin ta talabijin ranar Litinin da dare ya ce a baya-bayan nan kuma Lamine Zeine yana aiki ne da Bankin Raya Afirka a kasar Chadi a a matsayin masanin tattalin arziki.
A karshen watan Yuli ne sojoji suka yi wa Bazoum juyin mulki bayan ya shekara biyu da zaben sa, suka jingine kudin tsarin mulkin kasar mai yawan al’umma miliyan 26.
A karkashin mulkin Bazoum, Nijar ta kasance babbar kawa ga kasashen Yammacin duniya — Amurka, Faransa da Italiya — wajen yaki da masu ikirarin Jihadi a yankin Sahel.
A ranar Lahadi ne wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba wa masu juyin mulkin na dawo da Bazoum kan mulki ya kare, inda kungiyar ke duba yiwuwar daukar matakin soji, idan abin ya faskara.
Sojojin dai sun yi watsi da wa’adin na ECOWAS, inda a rana Lahadi suka rufe sararin samaniyar kasar tare da zama cikin shirin ko-ta-kwana.
Kasashen Guinea Bissau da Mali da Burkina Faso da ke hannun sojoji masu juyin mulki sun lashi takobin taimako da kuma yakar duk wanda ya yi kokarin yi wa takwarorin nasu na Nijar katsalandan.
Bayan wani taron da ECOWAS ta yi ranar Litinin bayan cikar wa’adain, a ranar Alhamis fira ministocin kungiyar za su yi wani a Abuja, babban birnin Najeria da ke shugabancin kungiyar domin cimma matsaya a kan mataki na gaba.
Amurka da Italiya dai sun bayyana cewa matakin diflomasiyya shi ne hanya mafi inganci wajen shawo kan rikicin na Nijar.
Sojojin sun ba wa dakarun Faransa umarnin ficewa daga kasar, amma Faransa, tsohuwar uwar gidan Nijar ta ce ba da su ta kulla yarjejeniyar tsaro ba, da halastacciyar gwamnatin Bazoum ta yi.
Sojojin dai sun kulla sabuwar yarjejeniyar tsaro da kamfanin sojojin haya na Wagner na kasar Rasha, wadda ba sa ga-maciji da Faransa da Amurka da ma kungiyar tsaro ta NATO.
Wagner Group ta fara aiki a Burkina Faso da Mali bayan da sojoji suka karbi mulkin kasar suka kuma sallami dakarun Faransa bisa zargin taimaka wa ’yan ta’adda.
Tuni Amurka da Faransa da Majalisar dinkin duniya da ke tallafa wa Nijar suka janye agajin nasu bayan juyin mulkin, a yayin da ECOWAS ta kakaba wa gwamantin sojin takunkumin karya tattalin arziki.
Najeriya, babbar makwabciyar Nijar ta katse wutar lantarkin da dake ba su, lamarin da ya jefa manyan biranen kasar cikin matsala.
A martaninsu kuma, gwamnatin sojin ta Nijar ta rufe iyakarta tare da katse huldar diflomasiyya da Najeriya.