Sojojin 196 sun ajiye aiki a Najeriya
Ana zargin ajiye aikin sojojin yana da nasaba rashin ƙwarin gwiwa a tsakanin sojoji, sakamon matsin rayuwa a ƙasar.
Aƙalla sojojin Najeriya 195 sun mika takardun ajiye aiki domin ƙashin kansu ga Rundunar Sojin Najeriya.
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ba ta bayyana dalilin ajiye aikin sojojin ba, amma wasu majiyoyi sun danganta lamarin da rashin ƙwarin gwiwa a tsakanin sojoji, sakamon matsin rayuwa a ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce Babban Hafsan Sojin rundunar ya amince da aniyar sojojin ta barin aiki domin ƙashin kansu.
Nwachukwu ya ce sojojin sun bi ka’ida kuma dokar aikin soji ta tanadi hakan, don haka, za su fara hutun barin aiki daga ranar 1 zuwa 24 ga watan Nuwamba, 2024.
- NAJERIYA A YAU: ‘Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta ‘Yan Najeriya Ajiye Aiki’
- Mutum 45 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Neja
Sanarwar da Birgediya-Janar O.H. Musa ya sanya wa hannu ta ce murabus ɗin sojojin zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan na Nuwamba.
wachukwu ya bayyana cewa rundunar ta yanke tattara jerin sojojin 195 da za su bar aiki don ƙashin kansu domin sallamar su a lokaci guda ne saboda ta yi musu kyakkyawan tsari kamar yadda ta saba a tsawon shekaru.
Ya ce hakan ya ba da damar bin dukkan ka’idoji da yin shirye-shiryen biyan su kuɗaɗensu na sallama da kuma fara karɓar fanshonsu.