Sojojin Amurka 100 sun sauka a Bauchi

DHQ ta jaddada cewa sojojin Amurkan masu ba da shawara da horo ne kawai, ba dakarun yaƙi ba ne.

Sojojin Amurka 100 sun sauka a Bauchi

Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta sanar da isowar kusan sojojin Amurka 100 tare da wasu kayayyaki a filin jirgin sama na Bauchi, domin ba da horo da tallafin fasaha ga Rundunar Sojojin Nijeriya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da babban jami’in yaɗa labarai na hedikwatar, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitara a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta ce aiko sojojin wani yunƙuri ne na aiwatar da tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka, bayan da Gwamnatin Tarayya ta nemi taimako a fannin horon soja, fasaha da musayar bayanan sirri.

Sai dai DHQ ta jaddada cewa sojojin Amurkan masu ba da shawara da horo ne kawai, ba dakarun yaƙi ba ne.

Haka kuma, ta ce za a gudanar da dukkan atisayen ƙarƙashin iko da jagorancin Gwamnatin Nijeriya tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojojin Ƙasa.

Haɗin gwiwar na da nufin ƙarfafa ƙwarewar sojojin Nijeriya wajen gano da murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci, tare da kare al’ummomin da ke cikin haɗari.

DHQ ta tabbatar wa ’yan ƙasa da cewa za ta ci gaba da bayar da sahihan bayanai kan wannan haɗin gwiwa na tsaro.