Sojojin Amurka 5 sun mutu a Afghanistan
Sojojin shida ne suka mutu a Afghanistan a wani hari da jirgin saman Amurka ya kai bisa kuskure, wanda shi ne hari mafi muni da ya rutsa da sojin Amurka a cikin shekara 13 da fara yaki a kasar.Cikin mutane shida da suka mutu sakamakon harin, biyar daga cikinsu Amurkawa ne, dayan kuma dan Afghanistan […]
Sojojin shida ne suka mutu a Afghanistan a wani hari da jirgin saman Amurka ya kai bisa kuskure, wanda shi ne hari mafi muni da ya rutsa da sojin Amurka a cikin shekara 13 da fara yaki a kasar.
Cikin mutane shida da suka mutu sakamakon harin, biyar daga cikinsu Amurkawa ne, dayan kuma dan Afghanistan ne.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana hakan ranar Talata, inda ta ce sojojin sun rasa rayukansu ne a wani hari da aka kai bisa kuskure a lardir Zabur, ranar Litinin.
Wani dan sanda, Ghulam Sakhi Rooghlawanay wanda ke gurin da al’amarin ya faru ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa harin ya auku ne a lokacin da aka kai hari kan wasu mayakan Taliban.
Wannan shi ne hari mafi muni da dakarun kungiyar kawance ta NATO suka taba kaiwa junansu bisa kuskure tun bayan mamayar da suka yi wa kasar a shekarar 2001.
A watan Afrilun shekarar 2002, wasu sojojin kasar Kanada hudu sun rasa rayukansu bayan da wani jirgin saman Amurka ya jefa masu bam a lardir Kandahar bisa kuskure. Hakazalika, sojojin Birtaniya uku sun mutu bayan wani hari bam a watan Agustan shekarar 2007 a lardin Helmand.