Sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama a Syria

Amurka ta ce wannan mataki da ta dauka ba shi da nasaba da Isra’ila.

Sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama a Syria

Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare ta sama wurare biyu da sojin juyin-juya-hali na Iran ke amfani da su a Syria.

A wata sanarwa da Sakataren Tsaron Amurka ya fitar Lloyd Austin, ya bayyana hare-haren na tsantsar kare kai.

Lloyd Austin ya ce martani ne ga jerin hare-haren da kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran suka fara kai wa dakarunta tun daga ranar 17 ga wannan wata na Oktoba.

Sun ce martani ne kan hare-haren da suke addabar sojin Amurka da ke Iraqi da Syria hare-hare.

Sama da mako guda da rabi kenan da sojin Amurka ke zafafa kai hare-hare kan kungiyar masu dauke da makamai da Iran ke marawa baya.

Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta ce an kai wa kawancen da Amurka ke jagoranta a Iraqi da Syria hari sama da sau 16 cikin wannan watan.

Sanarwar ta ce sai da ta aike da sako ga shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei a game da hare-haren da ake kai wa dakarun kasar a Gabas Ta Tsakiya a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya saboda yakin Isra’ila a Gaza.

Amurka ta ce wannan mataki da ta dauka a kan Iran da kungiyoyin da take mara wa baya a Syria ba shi da nasaba da Isra’ila, hasali ma ba ta tuntubi Isra’ilar ba kafin daukar sa.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC