Sojojin Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 207

Rundunar sojojin kasar Chadi ta fitar da sanarwa cewa ta kashe ’yan Boko Haram 207 a wani kauyen Najeriya da ke iyaka da kasar Kamaru da kuma Chadi. Rundunar sojojin ta fitar da sanarwar ne a ranar Talatar da ta gabata.Sanarwar ta bayyana a lokacin bata-kashi tsakanin sojojinta da ’yan Boko Haram a kauyen Garambu […]

Sojojin Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 207
Sojojin Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 207

Rundunar sojojin kasar Chadi ta fitar da sanarwa cewa ta kashe ’yan Boko Haram 207 a wani kauyen Najeriya da ke iyaka da kasar Kamaru da kuma Chadi.

Rundunar sojojin ta fitar da sanarwar ne a ranar Talatar da ta gabata.
Sanarwar ta bayyana a lokacin bata-kashi tsakanin sojojinta da ’yan Boko Haram a kauyen Garambu sojan kasarta daya ne ya rasa ransa, inda tara suka samu raunika.
Har zuwa yanzu ba a tabbatar da sahihin labarin ba duk da cewa rundunar kasar ta bayyana ta kwato wadansu kananan makamai da harsasai da kuma motaci biyu a hannun mayakan Boko Haram din.
Idan ba a manta ba kasar Nijar da Kamaru da Chadi sun hada gwiwa wajen taimaka wa Najeriya don a dakile ayyukan Boko Haram, inda a watan jiya ne kasar Chadi tare da taimakon Kamaru ta girke sojojinta don fatattakar Boko Haram da ke yunkurin shiga kasarta.
A watan jiya ne dai kungiyar Hadin kan Afirka ta amince a samar da sojojin hadin gwiwa, sannan ta bukaci majalisar dinkin duniya ta amince a kaddamar da hare-haren a kan ’yan Boko Haram.