‘Sojojin da aka kashe sun bar zawarawa masu juna biyu da marayu 21’

Tinubu ya bayyana cewa za a bai wa dakarun sojin da suka rasu lambar yabo ta ƙasa.

‘Sojojin da aka kashe sun bar zawarawa masu juna biyu da marayu 21’

Sojojin da wasu bata-gari suka kashe makonni biyu da suka gabata a Jihar Delta, sun rasu sun bar zawarawa da mata masu juna da kuma marayu.

Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana hakan ranar Laraba yayin binne dakarun sojin da suka riga mu gidan gaskiya a Abuja.

Ya bayyana cewa sojoji 17 da aka kashe a ranar 14 ga Maris, 2024, sun bar zawarawa 10 daga cikinsu akwai mata masu juna biyu 3 da kuma marayu 21.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Bola Tinubu, wanda shi ne babban baƙo na musamman a wajen bikin binne gawarwakin da aka yi a Maƙabartar Sojoji, ya bayyana cewa za a ba wa jami’an da suka rasu lambar yabo ta ƙasa.

Da yake jawabi muryarsa cike da jimami, Laftanar-Janar Lagbaja ya bayyana cewa a cikin mata uku masu juna biyu akwai mai dauke da cikin wata hudu da mai biyar da kuma mai cikin watanni takwas.

Lagbaja ya ce, “Mai girma [Shugaban Kasa], manyan baƙi, mata da maza, kisan Okuama ya ƙara wa sojojin Najeriya kulawa da kuma jihohin Najeriya.

“Daga cikin zawarawa 10 da suka rasu suka bari, akwai uku daga cikinsu na dauke da cikin wata  4 da mai 5 da mai 8. Sun bar marayu 21, da sauran wadanda suka dogara a kansu da suka haɗa da iyaye.

“A yayin da nake jajantawa iyalan waɗannan jaruman sojojin, ina tabbatar musu da cewa sojojin Najeriya da mutanen ƙasar nan nagari ba za su bar su haka kawai ba.

“Za mu yi iya ƙoƙarinmu don tallafa musu da kuma adana abubuwan tunawa da waɗanda suka rasu.”