Sojojin da suka tsere Kamaru sun dawo gida
Rahotanni daga Jihar Adamawa sun ce kimanin sojojin Najeriya 480 da suka tsere zuwa kasar Kamaru sun isa garin Mubi cikin yanayi na gajiya da kuma yunwa.Wani mazaunin garin Mubi ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan cewa ya ga sojojin a lokacin da ake sauke su a motoci wasu na dauke da makamai wasu […]
Rahotanni daga Jihar Adamawa sun ce kimanin sojojin Najeriya 480 da suka tsere zuwa kasar Kamaru sun isa garin Mubi cikin yanayi na gajiya da kuma yunwa.
Wani mazaunin garin Mubi ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan cewa ya ga sojojin a lokacin da ake sauke su a motoci wasu na dauke da makamai wasu kuma babu, yayin da wasu ke tafe da motoci masu sulke.
Wasu bayanan kuma sun ce an bai wa sojojin wadanda wasunsu ke sanye da kakin soji wasu kuma ke sanye da singileti abinci a wani sansanin soji da ke garin Mubi.
A ranar Litinin ne Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta cimma fahimtar juna da Kamaru kan dawo da sojojin gida, inda a sanarwar da ta fitar ta ce shiga cikin Kamaru da sojojin Najeriyar suka yi dabarar yaki ce kawai ba tserewa suka yi ba.
Lamarin ya biyo bayan kazamin fadan da aka yi ne tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da kuma sojojin Najeriyar a garin Banki da ke bakin iyaka a ranar Lahadi.
Hedkwatar sojan ta kara da cewa saboda dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ya sa dole aka kwance damarar sojojin Najeriya, domin tabbatar wa Kamaru cewa ba su da wata mummunar manufa gare ta.
Kakakin Rundunar Sojojin Kamaru, Kanar Didier Badjek ne ya fara tabbatar wa duniya cewa wasu jami’an tsaron Najeriya 480 sun ketara kan iyaka zuwa cikin Kamaru.
Ya shaida wa BBC cewa an karbe makaman jami’an tsaron na Najeriya, inda aka dauke su zuwa yankuna daban-daban na garin Marwa.
Wani mazaunin garin Gamboru ya ce ya ga rukunin wasu jami’an tsaro kimanin 50 akasarinsu ’yan sanda, a lokacin da suke tsallaka iyaka zuwa Kamaru.
Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade ya tabbatar wa Aminiya cewa sojojin sun dawo, amma ya ki fadin inda suke.
Daga baya Hedkwatar Tsaron ta ce sojojin da suka dawo daga Kamaru sun saurari jawabi daga Babban Kwamandan Runduna ta Uku Manjo Janar Zaruwa kuma za su kara gaba domin gudanar da wani aiki na yaki da ta’addanci. “Dukkan sojojin suna cike da karsashi kuma suna tare da cikakkun makamansu da kayan aikinsu,” inji Hedkwatar Tsaron.