Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bukaci taimakon Rasha

Hakan na zuwa ne yayin da ECOWAS ta ce za ta tura dakarunta kasar

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bukaci taimakon Rasha

Wasu shugabannin ECOWAS yayin taronsu a Abuja ranar LahadiECOWAS

Akwai fargabar yanayin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar ya dada dumama bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar sun nemi taimakon kasar Rasha a daidai lokacin da ECOWAS ke shirin tura nata dakarun don fatattakar su.

Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) dai wacce ke da goyon bayan kasashen Yamma da Majalisar Dinkin Duniya, ta ba sojojin wa’adin mako daya su dawo da hambararren Shugaban Kasa, Mohammed Bazoum kan kujerarsa, ko su fuskanci tsauraran matakai.

ECOWAS ta kuma bukaci Manyan Hafsoshin Tsaron kasashenta da su fara wata tattaunawa da nufin tsara hanyoyin da za su fara aiwatar da aikin sojojin na dawo da hambararriyar gwamnati.

Babban mai tsaron Fadar Shugaban Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, wanda aka fi sani da Omar Tchiani, ne dai ya ayyana kansa a matsayin sabon Shugaban Kasa, yayin da har yanzu suke ci gaba da tsare Bazoum a hannunsu.

Ko a ranar Asabar din da ta gabata sai da Kungiyar Kasashen Afirka (AU) ta ba sojojin na Nijar kwana 15 su koma barikokinsu sannan su dawo da gwamnatin farar hula.

To sai dai sojojin a cikin wata sanarwa da suka karanta a gidan talabijin din kasar ranar Lahadi, sun gargadi ECOWAS da kada ta kuskura ta tura dakarun nata cikin kasarsu.

Juyin mulkin dai wanda aka yi shi a ranar Larabar da ta gabata, ya sha suka  da Allah wadai daga kungiyoyi da kasashe da dama a fadin duniya, ciki har da daga kasar da ta yi wa Nijar din mulkin mallaka, wato Faransa.

Ita kuwa ECOWAS a nata bangaren wacce ta ce har yanzu Bazoum ta sani a matsayin Shugaban Kasa, ta kuma sanar da daukar wasu matakai a kan Nijar da suka hada da rufe kan iyakokin kasar na kasa da na sama da sauran kasashe.

Ta kuma haramta wa jiragen kasuwanci daga Nijar ko zuwa can tare da katse duk wata harkar ciniki tsakanin kasashe mambobinta da Nijar din.

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya