Sojojin Faransa: Dalilin da Janar Tchiani ya zargi Najeriya

Mazauna iyakar Najeriya da Nijar kuma sun nuna bacin ransu kan zargin Janar Tchiani na cewa Najeriya ta kafa sansanonin sojojin Faransa domin hana kasarsa zaune tsaye

Sojojin Faransa: Dalilin da Janar Tchiani ya zargi Najeriya

Abdourahmane Tchiani

An yi ca a kan Shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, saboda zargin Najeriya da gayyato sojojin Faransa domin hana kasarsa zaman lafiya.

’Yan Najeriya mazauna yankunan da Janar Abdurrahman Tchiani ya yi zargin an kafa sansanin sojojin Faransa da kuma masansa sun karyata zargin nasa, wanda jami’an diflomasiyya suka bayyana a matsayin babban abin kunya.

Mazauna iyakar Najeriya da Nijar kuma sun nuna bacin ransu kan zargin Janar Tchiani na cewa Najeriya ta kafa sansanonin sojojin Faransa a Dajin Gaba da ke Jihar Sakkwato da nufin hana kasarsa zaune tsaye, inda suka kwatanta zargin da ‘hirar teburin mai shayi,’ da zai iya kara dagula zaman doya da manja da ke tsakanin kasashen da a baya suke kamar tif da taya.

A wata hira da kafar yada labaran gwamnatin Nijar mai suna Radio-Télévision du Niger ta yi da shi a ranar Larabar da ta gabata ne Janar Abdurrahman Tchia ya zargi Najeriya na hada baki da Faransa domin hana kasarsa zaman lafiya.

Da yake karin haske kan zarge-zargen da ya yi a cikin shirin, Janar Ya kara da cewa bayanan sirrin da suka samu sun tabbatar da zuwan jojin kasar wajen a Dajin Gaba da ke Jihar Sakkwato.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta hannun Ministanta na Yada Labarai, Mohammed Idris, ta karyata zagin a matsayin mara tsuhe.

Yankunan kananan hukumomi biyar a Jihar Sakkwato — Gada da Gudu da llela da Sabon Birni da Tangaza, ne suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.

A kan haka ne wakilinmu ya ziyarci yankunan da ke kan iyakar kasahen biyu a Jihar Sakkwato, domin jin ta bakin mazauna, da nufin tabbatar da gaskiyar wannan dambarwa  wadda ta tayar da jijiyoyin wuya.

Babu Dajin Gaba a yankinmu — Al’ummar Sakkwato

Iyayen kasa da mazauna yankunan ta bangaren Najeriya sun bayyana cewa babu kamshin gaskiya a zargin nasa, domin kuma babu wani daji ko kauye da ke da wannan suna a daukacin yankin.

Sun bayyana masa cewa ba su taba ganin sojojin wata kasa a yanki nasu ba, kuma babu wani daji ko yanki mai sunan da Tchiani ya ambata.

Sun shawarci shugaban kasar ya guji yin zargin da ba shi da hujjoji domin kauce wa lalata dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta makwabtaka da ’yan uwantaka da al’adu da dai sauransu.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa sabanin zargin da Janar Tchiani ke yi, sojojin Nijar ne sukan shigo yankunansu kusan kowane dare inda suke aikin samar da tsaro tare da masu aikin tsaron sa-kai a yankunan.

Sun yi zargin cewa jami’an tsaron Nijar ba sa bari a tsallaka zuwa kasarsu, amma kan tsallako bangaren Najeriya ba tare da wata takura ba, har su cin zalin ’yan kasar su kwace musu kaya, sun masu kira ga Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki a kan lamarin.

A Karamar Hukumar Illella, Alhaji Abubakar Yusufu, Sarkin Arewan Araba, yankin da ke da nisan kilomita biyu daga yankin Konni na Jamhuriyar Nijar, ya yi fatali da zargin an kafa sansanin sojojin ƙasar waje a yankin illela ya shaida wa wakilinmu cewa babu wani ƙauye ko daji mai suna Gaba a yankin.

“Babu wani daji mai wannan suna a yankin Masarautar Araba ko ƙaramar hukumar Illela kuma babu wasu sojojin ƙasashen waje da muka gabi, saboda haka wanna maganar teburin mai shayi ne.

“Maimamakon haka ma sojojin Nijar ne ke zuwa garuruwan namu kowane dare. Suna zuwa su yi aiki tare da ’yan banganmu domin samar da tsaro a cikin al’ummominmu. Mu da mutanen Nijar ’yan uwa ne, babu mai raba mu da su,” in ji shi.

Da yake watsi da ikirarin shugaban kasar Nijar kan kafa sansanin sojojin Faransa a yankin illela, basaraken ya nuna fargaba cewa zargin na iya ƙara tsamin dangantaka tsakaninsu da makwabtansu na Nijar.

Ya ja hankalin shugaban na Nijar da cewa yin zargi mata tushe na iya dagula daɗaɗɗiyar dangantaka da hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen masu maƙwabtaka da juna ta fuskan al’ada da ’yan uwantaka.

Jami’an tsaron Nijar ke cin zalinmu

Shi ma wani mazaunin garin na Araba, Malam Muhammadu Danladi ya yi watsi da zargin da cewa shugaban Nijar ya yi ne domin bata sunan Najeriya.

“Karya ce, babu sojojin kasashen waje a yankinmu, zargin ba shi da tushe,” in ji shi.

Ya kuma koka bisa abin da ya kira cin zalin da sojojin Nijar ke wa al’ummomin yankin a watanni shida da suka gabata.

Ya ce, “Jimi’an tsaronsu sai cin zalinmu suke ci, suna ƙwace mana kaya haka kawai. Amma su da mutanensu babu mai takura su, su shiga su fita daga Najeriya babu mai ce musu komai. Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki.”

Wani dan caha a yankin da ya bayyana sunansa a matsyin Muhammad, ya karyata samuwar sojojin kasar waje.

Haka abin yake a yankin Tabanni Siddi da ke Karamar Hukumar Tangaza, inda mazauan suka shaida wa wakilinmu cewa babu wani daji ko gari ko kauye da ke da sunan Gaba, kuma babu sojojin kasar waje a yankunansu.

Dalilin zargin da Janar Tchiani ya yi

Shin me zai sa shugaban gwamnatin sojin Nijar yin irin wannan zargi mara tushe?

Wan masanin tarihi kuma kwararre a fannin tsaro daga Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato, Dakta Murtala Rufa’i, ya ce bincikensa kuma tattaunawarsa da al’ummomin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar sun suna babu gaskiya a zargin da Tchiani ke yi.

Dakta Murtala ya ce, “Na yi bincike kuma na tatatuna da mazauna yankunan da ke kan iyaka. Gaskiya babu inda sojojin Faransa suke. Kuma gaskiya mazauna yankunan ba su ji dadin abin da Tchiani ya yi ba.

“A tattaunawar da na yi da mazauna bangaren Najeriya da ke kan iyakar, sun bayyana rashin jin dadinsu da Tchian. Inda na fara zuwa bincike shi ne Karamar Hukumar Gada saboda na ji ya ambaci Dajin Gaba, don haka na yi zaton Gada yake nufi. Amma da muka je sai muka iske babu daji, sai dai hamada da ta hada karamar hukumar da iyakar Nijar.

A cewar Dakta Murtala Rufa’i, Tchiani ya yi zargin ne saboda fasa butun man kasarsa a ’yan ta’adda suka yi, amma ya kara da cewa, “Wanda ya fasa bututun shi ne Muhammad Saha, kuma Tchiani ya san shi farin sani.

Muhammad Salah shi ne asalin jagoran ’yan ta’addan Nijar daga kungiyar PFL, kuma sananne ne. Shi ne shugaban wata kugiya,kuma akwai zargin cewa Najeriya na taimaka masa.

“Ba na tunanin kasa kamar Najeriya da ke da dadaddiyar dangantaka da Nijar za ta yi irin wannan abu (ta kafa sansanin sojojin Faransa su suka taimakon ayyuka ta’addanci a Nijar.

“Dalili na biyu shi ne Najeriya ta ki goyon bayan gwamnatin sojin Nijar. Haka ECOWAS ba ta goyon bayansu, saboda haka Tchiani ke ganin ba za su zauna a inuwa daya da Najeriya ba.”

Dakta Murtala ya bayyana zargin a matsayin wata dabara ta kawar da hankalin jama’a daga matsalolin da suka addabi Nijar na talauci da rashin aiki da yunwa da kuma fushin al’ummar kasar.

Don haka ya bukaci Janar Tchiani ya yi kokarin magance matsalolin ta’addanci da yunwa da talauci da dangoginsu da suka addabi Nijar maimakon neman dora wa wani laifi.

Labarin kanzon kurege ne —Janar Musa

Shi ma Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi watsi da zargin na Janar Tchiani a matsayin soki-burutsu, yana mai cewa Najeiya ba ta da niyyar kafa sansanin sojojin kasashen waje.

A ziyarar da ya kai Sakkwato a baya-bayan nan, Janar Christopher Musa ya ce, “Ina amfani da wannan dama in shaida wa makwabtanmu: Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin da Togo, cewa Najeriya ba za ta bar duk wani mai laifi kodan ta’adda ya yi amfani da doron kasartas domin kai wa ko daya daga cikinsu hari ba.”

Tchiani ya zubar da kimarsa —Jami’in diflomasiyya

Tsohon jami’in diflomasiyya, Ambasada Sulaiman Dahiru, a yayin hirars da tashar Trust TV, ya soki shugaban na Nijar kan zargin da ya yi ba tare da wata hujja ba.

“A tunani na ya riga ya zubar wa kansa kima a wannan zamani na fasaa. Idan da wani karamin jami’in soji ne ya yi irin wannan zargi daga Nijar da abin da sauki. Amma shugaban kasa sukutum ya yi irin wadannan maganganu, wannan babban abin kunya ne.

“Ina ganin muddin zai ci gaba da zama a ofis, dangantakar kasashen biyu ba za ta koma yadda take ba. Tsawon shekaru an yi gwamnatocin soji da na farar hula a Nijar, kuma duk da haka alaka tsakanin kasashen tana tafiya lafiya kamar ’yan uwa.

“Na taba fadin cewar idan kana zauna a Arewacin Najeriya kusan babu bambanci da Nijar. Dangantakar da ta hada mu ta addini da al’ada ce da sauransu. Babu abin da zai raba Najeriya da Nijar, don haka dole ne kasashen su san yanda za su zauna da juna lafiya,” a cewar Ambasada Suleiman Dahiru.

Tsohon kwamishina ya caccaki shugaban Nijar

Ex-Adamawa commissioner hits Nigerien ruler

A former Commissioner for Information in Adamawa State, Ahmed Sajo, described the allegations by Tchiani as “showmanship.”

Ahmed Sajo ya ce, “abin takaicin shi ne yadda ’yan Najeriya ciki har da wasu nagartattun kungiyoyi suke goyon bayan wannan adawar, har suke amfani da ita suna dora alamar tambaya kan nagartar gwamantin kasarsu.

“Idan aka lura da yadda abubuwan ke faruwa an tsara su ne da nufin jawo wa gwamnatin Najeriya bakin jini a tsakanin ’yan Nijar, wanda kuma hakan zai shafi Arewacin Najeriya. An tsara kuma an aiwatar da su da harshen Hausa maimakon Faransanci, wanda shi ne harshen da Nijar ke amfani da shi a hukumance.

“Domin abin nasu ya yi kamar gaske sai ya yi amfani da sunayen manyan mutane biyu masu daraja da fannin tsaron Najeriya; Ahmed Abubakar Rufai wanda tsohon Shugaban Hukumar Tsaron Soji ne, sai kuma Nuhu Ribadu, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro a halin yanzu.

“idan aka dauki batun Lakurawa alal misali sanin kowa ne cewa daga Mali suka fito suka shigo Najeriya. Amma ai Najeriya ba ta hada iyaka da Mali ba, duk mai zuwa Najeriya daga Mali sai ya ratsa ta Nijar.

“To yaya mutumin da ya ba wa ’yan ta’adda hanya suka ratsa ta kasarsa zai zo yana zargin wani yana amfani da su wajen tayar da zaune tsaye a kasar tasa? Shin wannan sai an yi  dogon tunani?”

Zargin da Tchiani ya yi babu hujja — Cote D’Ivoire

Babban Hafsan Tsaron kasar Côte d’Ivoire, Janar Lassina Doumbia, a ranar Asabar ya sanar da cewa zargin da Janar Tchiani ya yi na horas da ’yan kasarsa domin tayar wa gwamnatinsa kayar baya ba shi da tushe balantana hujja.

A sanarwar da ya fitar, Janar Doumbia ya shawarci gwamnatin sojin Nijar ta dauki matakan magance matsalolin tsarron kasar na cikin gida.

“Rundunar Tsaron Kasar Côte d’Ivoire, wadda ke aiki haikan wajen tabbatar da tsaron al’ummar kasar ta yi watsi da zargi mara tushe mara dalili da shugaban gwamnatin sojin Nijar ya yi.

“Rundunar Tsaron Côte d’Ivoire tana tsaye kai da fata kan tsohon alkawarin hadin kai da kasashen da ke yankin Yammacin Afirka kuma za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen wanzar da aminci da kwanciyar hankali a yankin,” in ji shi.

 

Daga: Abubakar Auwal da Dalhatu Liman da Sagir Kano Saleh