Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta a Lebanon

Dakarun na Isra’ila sun tabbatar da da kai harin ne a sansanin soji da ke Naqoura.

Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta a Lebanon

Wani yanki na birnin Beirut da ke Lebanon da harin ya shafa

Dakarun Isra’ila sun yi luguden wuta a yankun da mayakan Hezbollah ke zama a Kudancin Lebanon, a daidai lokacin da rikici ke kara rincabewa a iyakar kasashen.

Dakarun na Isra’ila sun tabbatar da da kai harin ne a sansanin soji da ke Naqoura, bayan harba wasu rokoki da aka yi daga yankin da kuma ya fada cikin Isra’ilar.

A cewar sojojin na Isra’ila dai, sun afka wa mazaunin mayakan Hezbollah ne yayin kuma da ma’aikatar tsaron kasar Lebanon ke cewa hare-haren ramuwar gayya daga Isra’ilar a wannan Laraba, sun fada ne kan wasu kauyuka da ke iyakar kasashen biyu.

Kafofin sadarwa a Lebanon sun ruwaito cewa, Nabgh al-Qaderi, dan kungiyar Resistance Brigades mai alaka da Hezbollah, ya mutu a harin na jirgi mara matuki da Isra’ilar ta kai a wani gida a garin Kfar Shuba.

A wani labarin kuma, Ma’aikatar lafiya da kungiyar Hamas da ke karkashin Hamas a Zirin Gaza, adadin wadanda suka mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sakamakon luguden wuta daga Isra’ila sun kai 147.

Tun bayan fara yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas dai, yanzu jami’an fararen hula dubu 23 da 357 suka rasa rayukansu

Adadin kuma wadanda suka jikkata, su ne mutum dubu 59,410.

Ana iya tuna cewa, a ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki ne kungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugabanta a Lebanon, Saleh al-Arouri, a harin da aka kai a Kudancin birnin Beirut.

An ce al-Arouri na cikin shugabannin ayyukan Hamas na soja.

Wani babban jami’in tsaro a Beirut ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, an kashe Aruri da wasu masu tsaronsa ne a wani hari da Isra’ila ta kaddamar a yankin unguwar Dahiyeh da ke zama kakkarfar tungar mayakan Hezbollah mai kawance da Hamas.

Gidan talabijin na gwamnatin Lebanon ya ce mutanen da suka mutu a harin da ya kashe mataimakin shugaban Hamas a Lebanon sun kai shida.