Sojojin Kamaru sun kashe ’yan Boko Haram 40
Dakarun Kamaru sun kashe kusan’yan kungiyar Boko Haram 40 a wata musayar wuta da suka yi a garin Fotokol mai iyaka da Najeriya a lardin Arewa-mai-nisa, ranar Litinin.Wannan ya faru ne a wani yunkurin da ’yan Boko Haram suka sake yi na karya gadar da ta hada garin Gamboru a Najeriya da Fotokol da ke […]
Dakarun Kamaru sun kashe kusan’yan kungiyar Boko Haram 40 a wata musayar wuta da suka yi a garin Fotokol mai iyaka da Najeriya a lardin Arewa-mai-nisa, ranar Litinin.
Wannan ya faru ne a wani yunkurin da ’yan Boko Haram suka sake yi na karya gadar da ta hada garin Gamboru a Najeriya da Fotokol da ke Kamaru, inda jama’a suke ta tserewa domin kubuta da rayukansu.
Har ila yau, akwai wasu daruruwan ’yan gudun hijira da keta shiga garin Amchide a Kamaru sakamakon mamaye garin Bama da ’yan Boko Haram din suka yi tun da farko. Jama’a da dama da Aminiya ta tuntuba sun tabbatar da cewa sun gane wa idanunsu dimbin gawawwakin da suke kwance akan tituna ba tare da sauran ’yan uwansu sun kawar da su ba.
Baya ga haka kuma, jami’an tsaro sun kona wasu motoci biyu da wadanda maharan suka zo da su. Daga bangaren jami’an tsaro kuwa, akwai wani soja guda da tartatsin albarushi ya shafi jikinsa, sai dai bisa ga sanarwar jami’an tsaro, sojan na samun kula a wani asibiti da ke birnin Maroua.
Wadanda arangamar ta faru akan idansu sun ce, bangarorin biyu sun kwashe kimanin sa’a uku suna artabu. Wanda sakamakon wadannan tashe-tashen hankulan dubban jama’a ne suke tururuwa daga Najeriya suna ketarawa Kamaru, masamman ma tun bayan da aka bayyana bullar ’yan Boko Haram a garin Bama suke ta tserewa suna zuwa Banki har ma wasu garuruwa kamar Mora da kuma Maroua. Hakan ya sa gwamnatin Kamaru neman taimako daga hukumar kula da ’yan gudun hijira da kuma hukumar jin kan jama’a domin su taimaka mata wurin karbar ’yan gudun hijiran da suke ta yin tururuwa tsakanin garuruwan kan iyakar kasashen biyu.