Sojojin Najeriya sun kashe masu kera bom din Boko Haram
An kashe ’yan ta’adda 38 ciki har da sabon shugaban kungiyar ISWAP.
Sojojin Najeriya sun hallaka masu hada wa kungiyar Boko Hara bom a samamen da suka kai wa maboyarsu a Jihohin Borno da Yobe.
Sojojin rundunar Operation Hadin Kai da suka kai samamen sun kuma kwace motoci biyu tare da buhu 622 na takin zamani da Boko Haram take amfani da su wajen hada abubuwan fashewa.
- Ban gamsu da shirin gyara halin tubabbun ’yan Boko Haram a Gombe ba —Gwamna
- Dogo Gide ya hallaka Damina, kasurgumin dan bindigar da ya addabi Zamfara
Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce, “An kashe ’yan ta’adda 38 da suka hada da sabon shugaban kungiyar ISWAP, Malam Bako da mayakansa.
“An kwace motocin yaki 2 da buhu 622 na takin zamanin da ake hada abubuwan fashewa da su, sai manyan makamai 29 da harsasai 166, aka kuma kubutar da fararen hula biyar da aka yi garkuwa da su.
“Mutum 11 da suka hada da ’yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka da masu kai musu bayanai da masu yi musu jigilar kaya sun shiga hannu,” a samamen da sojoji suka kai.
Ya bayyana a ranar Alhamis cewa ’yan Boko Haram din sun gamu da gamonsu a hannun sojojin ne a kauyukan, Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da kuma Kijmatari, duk a Jihar Borno.
Wasu kuma sun gamu da ajalinsu ne a kan titin Ngala zuwa Wulgo na jihar, sai kuma a kan hanyar Nguru zuwa Kano a Jihar Yobe.