Sojojin Najeriya sun kashe ’yan Boko Haram fiye da 300

Hukumomin sojan Najeriya sun ce sun kashe ’yan Boko Haram sama da 300 tare da kame wasu da dama a yakin da suka kaddamar kan mayakar kungiyar a yankin Arewa maso Gabas. Kakakin Hedkwatar Tsaro ta kasa, Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan a shekaranjiya Laraba cewa an samu nasarar […]

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan Boko Haram fiye da 300
Sojojin Najeriya sun kashe ’yan Boko Haram fiye da 300

Hukumomin sojan Najeriya sun ce sun kashe ’yan Boko Haram sama da 300 tare da kame wasu da dama a yakin da suka kaddamar kan mayakar kungiyar a yankin Arewa maso Gabas.

Kakakin Hedkwatar Tsaro ta kasa, Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan a shekaranjiya Laraba cewa an samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram din ne sakamakon ruwan wuta da ake yi musu ta sama da kasa a kwanaki biyun da suka gabata.
Ya ce an kama dimbin makamai da sauran kayayyakin aiki tare da lalata wasu a lokacin farmakin.
Janar Olukolade ya ce an kwato tankokin yaki biyar da bindigar harbor jiragen yaki daya da akwatunan bama-bamai 50 da nau’o’in bindiga mai sarrafa kanta guda takwas da kuma rokokin harba gurneti guda biyar a lokacin farmakin.
Ya ce har wa yau an lalata akwatunan 49 da ke dauke da harsasai iri-iri da babura 300 da motoci kirar Hilud shida ciki har da wadanda ke dauke da bindigogin harbor jiragen sama.
Janar Olukolade ya ce, “gawurtaccen” farmakin da sojojin Najeriya suke kaiwa zai ci gaba, har sai an tabbatar jama’ar garuruwa 11 da suka hada da Monguno da Gabchari da Abba Jabari da Zuntur da Gajigana da Gajiram da Damakar da Kumaliwa da Bosso da Wanti da Jeram da kuma Kabrisungul da a yanzu sojoji suka mamaye su, sun tsira daga mayakan Boko Haram.
Kakakin ya ce sojoji biyu sun mutu a yayin artabun yayin da 10 suka samu rauni. Kuma ya ce an tsara kai farmaki iri daban-daban da sojojin ke gudanarwa a sabon shirin yaki da ’yan ta’addan da aka kaddamar a ciki da wajen Najeriya.
A ranar Litinin ne hukumomin sojan suka ce sun sake kwato garin Monguno da wasu garuruwa daga mayakan Boko Haram.
Makonni shida da suka gabata ne mayakan Boko Haram suka kai hari da sassafe garin na Monguno mai nisan kilomita 137 daga Maiduguri, fadar jihar, inda suka kwace garin makonni biyu da suka gabata.
Kame Monguno da garuruwan da ke kusa ya matso da Boko Haram kusa da Maiduguri, sai dai sojoji sun rika samun nasarar dakile mayakan kungiyar daga yunkurinsu na shiga Maidugurin.