Sojojin Najeriya za su iya ceto ’yan matan Chibok – Babangida
Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana da yakini sojojin Najeriya na da kwarewar da za su iya kubutar da ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram ke ci gaba da tsare su fiye da kwana 120 da sace su.Janar Ibrahim Babangida ya bayyana haka ne a gidansa a Minna lokacin da […]
Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana da yakini sojojin Najeriya na da kwarewar da za su iya kubutar da ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram ke ci gaba da tsare su fiye da kwana 120 da sace su.
Janar Ibrahim Babangida ya bayyana haka ne a gidansa a Minna lokacin da ya gana da manema labarai bayan da aka gudanar da addu’o’in cikarsa shekara 73 a duniya.
Tsohon Shugaban kasar ya kara da cewa, “Al’amari irin wannan na da matukar tsauri, bari in ba ku misali da Yakin Basasa. Babu wanda ya yi tsammanin za a yi gwagwarmaya na tsawon shekara uku. Sai ga shi an dauki wannan lokacin kafin a kai ga nasarar kawo karshen lamarin. Don haka sojojin da kuke gani kwararru ne, ya kamata a ba su lokaci za su ba mara da kunya.”
Da ya juya kan rawar da sojoji ke takawa yayin gudanar da zabuka ya ce, ba daidai ba ne a rika ba sojoji alhakin kula da yadda ake gudanar da zabe a kasar nan.Ya ce ana iya tura su wuraren da ake gani ko shakkar ana iya tayar da zaune-tsaye da zai iya kai ga asarar rayuka.
Ya ce ana samun ci gaba da ingantuwar yadda ake gudanar da zabubbukan shugabannin da za su ja ragamar wannan kasa a dukkan matakai idan aka auna yadda aka fara tafiyar zaben wannan jumhuriyya daga 1998 zuwa yanzu.
Game da sake tsayawa takarar Shugaba Jonathan a shekarar 2015, Janar Bababngia ya ce tsarin mulki bai haramta masa neman wani wa’adin ba, don haka bai zama laifi ba kuma ya kamata a rika yi wa tsarin mulkin karatun ta-natsu.
Ya yi fatan ’yan Najeriya za su yi amfani da kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu don daura damarar ciyar da kasar gaba, inda ya ce lokaci ya yi da za a kauce wa yada bambance-bambancen addini ko na kabilanci a fuskanci batun bunkasa kasar nan wadda Allah Ya yi wa dimbin albarkaru da jama’a masu ilimi da hikima da basira.
Da yake tsokaci game da cikarsa shekara 73 a duniya, ya yi godiya ga Allah da Ya nuna masa wannan rana cikin da koshin lafiya, kuma a cikin Ya ce, a cikin ’ya’ya da jikokinsa. Ya gode wa ’yan uwa da abokan arziki da sauran wadanda suka bayar da gudunmuwa ta kowace fuska aka tara malamai domin yi masa addu’o’in taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.