Sojojin Nijar sun bukaci a fitar da jakadan Faransa ta karfin tsiya

Sun ce sun janye masa duk wasu abubuwa a matsayin jakada

Sojojin Nijar sun bukaci a fitar da jakadan Faransa ta karfin tsiya

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron

Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun bayar da umarnin fitar da jakadan Faransa a kasar, Syvain Itte, ta karfin tuwo.

Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ce ta bayar da umarnin ranar Alhamis.

Sojojin dai da suka kifar da Gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum, a watan da ya gabata, sun ba jakadan sa’o’i 48 ya bar kasar a makon da ya gabata.

Sai dai wa’adin ya kare ranar 28 ga watan Agusta, ba tare da kasar ta Faransa ta kira shi ba, saboda ta ce gwamnatin sojojin haramtacciya ce.

A ranar Litinin, shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a ranar Litinin ya ce jakadan zai ci gaba da zama a kasar duk da barazanar da sojojin suka yi.

Sabuwar sanarwar sojojin na Nijar dai ta ce daga yanzu za ta janye wa jakadan duk wasu abubuwa da yake mora a kasar.

Sun kuma ce za a janye duk wasu takardun diflomasiyya sannan za ta soke bizar shi tare da ta iyalansa.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Bazoum dai, sojojin ke ta kirkiro dokokin da suke yakar manufofin Faransa a kasar.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano