Sojojin Nijar sun kama jagoran ’yan bindigar Najeriya

Sojojin Nijar sun kama Kachalla Mai Daji yana kokarin sace dabbobi ya tsallaka iyakar Najeriya da Nijar

Sojojin Nijar sun kama jagoran ’yan bindigar Najeriya

Masu neman shiga aikin sojin sa-kai a Nijar a inda suka taru a filin wasa na Janar Seyni Kountche da ke birnin Yamai ranar Asabar 19 ga Agusta, 2023.
(Hoto: AFP)

Dakarun sojin Jamhuriyar Nijar sun kama wani jagoran ’yan bindigar Najeriya, Kachallah Mai Daji a kusa da iyakar garin Illela da ke kasar.

Masanin harkar tsaro kuma mai sharihi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin Nijar sun kama dan bindigar ne a lokacin da yake kokarin sace dabbobi ya tsallaka iyakar Najeriya da Nijar da su.

“Sojojin Nijar sun damke shi yana kokarin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar,” in ji shi.

Zagazola ya bayyana Kachallah Mai Daji a matsayin daya daga cikin hatsabiban yan bindiga da suka shafe shekaru suna addabar yankin Arewacin Najeriya.

A cewarsa, “dan ta’addan ya shafe kusan shekara 10 yana kashe mutane da kona kauyuka da sace jama’a da ma kakaba musu haraji a kauyukansu.”

Kachalla Mai Daji dai ya fi addabar kauykan yankin Illela da suka hada da Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Ɗan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da sauran makwabtansu.

Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas 

Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144

Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq

Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba