Sojojin Nijar sun yi kunnen uwar shegu da wa’adin ECOWAS

Ba san matakin da ECOWAS za ta dauka ba a nan gaba

Sojojin Nijar sun yi kunnen uwar shegu da wa’adin ECOWAS

Tinubu da wasu shugabannin ECOWAS

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi kunnen uwar shegu da cikar wa’adin da ECOWAS ta ba su na su mayar da mulki ko ta afka musu da yaki.

A makon da ya gabata ne dai Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ta ba sojojin wa’adin mako daya na su dawo da hambararren Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum, kan karaga, ko kuma ta tura musu nata sojojin.

To sai dai bayan cikar wa’adin ranar Lahadi, har yanzu sojojin sun kekashe kasa kan barazanar ta ECOWAS, inda a yanzu ma suke samun tallafin fararen hula wajen gadin manyan biranen ƙasar irin su Yamai da Maradi, saboda shirin ko ta kwana.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa kimanin mutum 30,000 ne suka taru a wani filin wasa na birnin Yamai suna daga tutar kasar Rasha, yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar abin da ka iya faruwa a yanzu.

Kafar ta ce daga bisani jami’an gwamnatin mai ci sun isa wajen ranar Lahadi domin karfafa musu gwiwa.

Sai dai har yanzu, gwamnatin sojin ba ta fitar da wata sanarwa ba kan cikar wa’adin.

Wakilanmu wadanda yanzu haka ke kan iyakokin Najeriya da Nijar a Jihohin Sakkwato da Katsina da Jigawa da Borno, sun lura kodayake babu fada, amma mutane na cikin barazanar rashin tabbas din abin da zai iya faruwa, sakamakon tsadar abinci da sauran kayan masarufi.

Mazauna yankunan na kasashen biyu sun ce ba sa son yaki inda suka yi kira ga ECOWAS din da ta sauya tunani.

Ko a daren Lahadi dai sai da Shugaba Tinubu ya gana da Gwamnonin jihohin da suka hada iyaka da Nijar din na Sakkwato da Jigawa da Yobe da da Kebbi da kuma Katsina.

To sai dai ya zuwa yanzu babu wani karin bayani daga Fadar Shugaban Kasa kan abin da suka tattauna, ko mataki na gaba da ECOWAS za ta dauka a kan lamarin.

Kazalika, wakilanmu sun lura cewa an tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin Najeriya da Nijar na Illelah a Sakkwato da Jibiya a Katsina da kuma Maigatari a Jigawa.

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno