Sojojin Rasha sun harbe dan jaridar Amurka a Ukraine
Wannan ne karon farko da aka samun labarin kashe dan jarida a yakin Rasha a Ukraine.
Rahotanni daga kasar Ukraine sun ce an harbe wani dan jaridar Amurka Brent Renault tare da jikkata wani ranar Lahadi a Irpin, kusa da Kyiv, babban birnin Ukraine.
Wannan na zuwa ne a yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Ukraine da na Rasha ya kazanta, a yankin da ke Arewa maso Yammacin birnin Kyiv, kamar yadda likitoci da shaidu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
- Mustafa Shehu: Mutumin Kano da ya zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya
- Ban fita daga PDP ba tukunna —Kwankwaso
Wasu bayanai sun ce an kuma raunata wasu ’yan jarida biyu da suke tare da shi.
Wannan ne karon farko da aka samun labarin kashe dan jarida a yakin Rasha a Ukraine.
BBC ya ruwaito cewa dan jaridar yana tare da katin shaida na jaridar New York Times a tare da shi.
Ba a tantance kafar yada labaran da dan jaridar ya ke aikawa rahotanni ba a yakin Ukraine.