Sojojin sama sun cafke jagoran ’yan bindiga a Kano
Rundunar sojin saman Najeriya ta kama wani jagoran masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Rundunar sojin saman Najeriya ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Jihar Kano.
An kama jagoran ’yan bindigan ne a samame da sojoji suka kai maboyarsa da yaransa da ke Karamar Hukumar Takai.
Ana zargin gungun ’yan ta’addan ne suka addabi yankin karamar hukumar da garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya ce bincike ya nuna cewa Isah Abdul da gungunsa ne suka sace wani mai suna Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda aka fi sani da “Sarkin Noman Gaya,” a ranar 6 ga Afrilu, 2023.
- Yunwa: Jama’a sun daka wa motar Dangote wawa a Katsina
- Hisbah ta cafke ’yan kasar waje kan aikata badala a Kano
An sace Sarkin Noma Gaya ne a kauyen Tagaho a ranar 6 ga watan Janairu.
Ya kara da cewa an sako wanda aka sacen bayan wata guda bayan an biya kudin fansa N30,000,000.