Sojojin Saudiyya sun dakile harin mayakan Houthi

Dakarun Rundunar da kasar Saudiyya ke jagoranta wurin yaki da ’yan tawayen Houthi sun dakile harin kungiyar a ranar Juma’a. Dakarun ahdin gwiwar sun ce sun tarwatsa wani jirgin ruwa makare da ababen fashewa a kan Tekun Bahar Maliya. ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’ Yadda kama almajirai a gidan Sheikh Dahiru Bauchi ke […]

Sojojin Saudiyya sun dakile harin mayakan Houthi

Kakakin Rundunar Kawancen Kasashen Larabawa, Kanar Turki Al-Maliki

Dakarun Rundunar da kasar Saudiyya ke jagoranta wurin yaki da ’yan tawayen Houthi sun dakile harin kungiyar a ranar Juma’a.

Dakarun ahdin gwiwar sun ce sun tarwatsa wani jirgin ruwa makare da ababen fashewa a kan Tekun Bahar Maliya.

Gidan Talabijin na kasar Saudiyya, Ekhbariya ya ce dakarun sun kuma tarwatsa wasu jiragen yaki marasa matuka na ’yan Houthi da suka yi yunkurin kai hari a Saudiyya.

Tun shekarar 2015 Rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagorantar yaki da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan ’yan tawayen na Houthi.

’Yan Houthi na ta kai hare-haren rokoki a kan yankunan kasar Saudiyya daga kasar Yemen.

Kasar Yemen ta jima tana fama da rikin ’yan Houthi da ke yakar gwamantin kasar wadda ke da goyon bayan Saudiyya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa