Sojojin Siriya sun kwace tsohon birnin Aleppo

Sojojin gwamnatin Siriya sun kwace yanki na karshe da ‘yan tawaye ke rike da shi a tsohon birnin Aleppo mai cike da tarihi, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a kasar ta sanar. kungiyar mai cibiya a Birtaniya ta kara da cewa, ‘yan tawayen sun fice ne bayan sojojin sun […]

Sojojin Siriya sun kwace tsohon birnin Aleppo
Sojojin Siriya sun kwace tsohon birnin Aleppo

Sojojin gwamnatin Siriya sun kwace yanki na karshe da ‘yan tawaye ke rike da shi a tsohon birnin Aleppo mai cike da tarihi, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a kasar ta sanar.

kungiyar mai cibiya a Birtaniya ta kara da cewa, ‘yan tawayen sun fice ne bayan sojojin sun danna su a cikin daren da ya gabata.
Wannan kuma na zuwa ne bayan yankin ya shafe tsawon shekaru hudu a karkashin ikon ‘yan tawayen, inda suka ci karensu babu babbbaka.
Yanzu haka dai, fiye da kashi biyu bisa uku na gabashin Aleppo na karkashin ikon gwamnatin Siriya, yayin da ta ke ci gaba da kokarin karbe birnin baki daya.
Kimanin fararen hula dubu 80 ne suka kaurace wa yankin gabashin Aleppo tun bayan da sojoji suka kaddamar da farmakin kwace shi daga hannun ‘yan tawaye a cikin tsakaiyar watan Nuwamban da ya gabata.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara