Sojojin sun kashe shanu 74 a Kaduna
Rahotanni daga rugar Fulani a kauyen Riyawa a Sabon Birni da ke Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna na cewa, akalla shanu 74 ne sojoji suka kashe. Wani mazaunin garin Sanusi Bara, ya bayyana wa majiyarmu cewa, a ranar 17 ga watan Nuwamba 2018 da misalin karfe 6:00 na safe sojojin suka shiga garin Riyawa […]
Rahotanni daga rugar Fulani a kauyen Riyawa a Sabon Birni da ke Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna na cewa, akalla shanu 74 ne sojoji suka kashe.
Wani mazaunin garin Sanusi Bara, ya bayyana wa majiyarmu cewa, a ranar 17 ga watan Nuwamba 2018 da misalin karfe 6:00 na safe sojojin suka shiga garin Riyawa suka kashe shanu 74 tare kone gidaje uku da kuma kona hatsin da aka girbe.
Darekta mai rikon kwarya na watsa labaran jami’an tsaron sojojin Birgediya Janar John Agim, ya bayyana wa manema labarai cewa garin Riyawa na daya daga cikin garin da barayin shanu da masu garkuwa da mutane ke boyewa.